More Podcasts
Yanzu wata guda ke nan tun bayan da jirgin sojoji ya yi kuskuren kai hari kan masu taron Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin da kuma bayyana matakan da za a bi wajen kwato hakkin waɗanda lamarin ya shafa.
- DAGA LARABA: Abin Da Zai Faru Idan Mutum Ya Cika Cin Goro
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Samun Kuɗi A 2024
Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina kudaden da aka tara na tallafi suke?
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari na musamman a kan matakin da ake kai na bincike kan harin.
Domin sauke shirin, latsa nan