✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada sabon shugaban EFCC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban riko na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC bayan dakatar da Ibrahim Magu nan…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban riko na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC bayan dakatar da Ibrahim Magu nan take.

Buhari ya nada Darektan Ayyukan EFCC, Mohammed Umar, ya ci gaba da rike hukumar har a kammala binciken zargin da Magu ke fuskanta.

“Ya kuma nada Darektan Ayyuka na EFCC Mohammed Umar, ya rike hukumar zuwa lokacin da kwamitin zai kammala bincike da kuma umarnin da zai biyo baya”, inji sanarwar Ministan Shari’a.

Sanarwar kakakin ministan, Umar Gwadu ta ce dakatarwar “za ta ba kwaminitin binciken da shugaban kasa ya kafa cikakkiyar damar gudanar da aikinta yadda doka ta tanada.

Rahotanni sun ce an kafa kwamitin ne bayan takardar zargin almundahana da Malami da kuma hukumar tsaro ta DSS suka aike wa Buhari kan Magu.

Magu na faukantar zargi 22 kan sakaci da aiki da kawo wa ofishin Ministan Shari’a cikas da yi masa danwaken zagaye, da kuma rashin bayar da gamsassun bayanai kan kadarorin gwamnati da aka kwato daga mutane.

Sai dai a baya Malami ta bakin mai magana da yawunsa ya musanta aikewa da takardar. Gwandu ya kuma ce ba shi da masaniya game da tsare Magu bisa zarge-zargen.

Sai dai kuma da wakilinmu ya tuntubi ministan yada Labarai Lai Mohammed game da lamarin, sai ya ce masa Ministan Shari’a ne zai yi magana a kan batun ba shi ba.

Rahotanni sun ce jami’an DSS sun yi wa Magu dirar mikiya ne suka tisa keyarsa zuwa gaban kwamitin da ke zama a fadar Shugaban Kasa, wanda tun daga sannan babu takamaiman bayani game da inda shugaban na EFCC yake, ko matsayinsa.

Sai dai fadar shguaban kasa ta ce ba tsare Magu aka yi ba, gayyatar sa aka yi domin ya amsa tambayoyin kwamtintn.

Batun binciken Magu wanda ake wa lakabi da sarkin yakin cin hanci da rahawa na gwamnatin Buhari ya tayar da kura a Najeriya, inda jam’iyyar adawa ta PDP da masu ra’ayi irin suka yi ta kira da ya sauka daga kujerasa domin a yi cikakken bincike.

A bangare guda kuma, magoya bayan wanda ake binciken na kallon zargin a matsayin kutungwila, suna masu kafa hujja da yadda aka juma ana kokarin ganin Buhari bai nada shi cikakken shugaban EFCC ba.

Ita kuma jami’iyyar APC da gwamnatinta na tutiyar cewa binciken manuniya ce da ke tabbatar da babu shafaffe da mai a yaki da take yi da rashawa.

Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam a kasar sun ce, duk da cewa suna goyon bayna a yi bincike, suna kira da ayi gaskiya da adalci a binciken da kuma yanke hukunci.