Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da ’yan Najeriya cewa daga satar daliban Makarantar Sakandiren Gwamnati ta ’Yan Mata dake Jangebe a a jihar Zamfara ba za a sake sace dalibai a makarantu ba.
Tabbacin na Shugaban Kasa na kunshe ne cikin sakonsa da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya isar yayin da ya jagoranci wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya domin jajantawa Gwamnati da al’ummar jihar Zamfara a kan iftila’in.
- Ba mu san ranar sake bude makarantun da muka rufe ba – Gwamnatin Neja
- An kama shi da hodar iblis ta biliyan 1 yana kokarin tsallake kasa ta Sakkwato
Ya ce gwamnatin ta fito da managartan matakai domin kawo karshen kowanne irin nau’i aikata laifi a kasar.
“Shugaban Kasa ya damu matuka da sace wadannan daliban na Jangebe, kuma yana ba da tabbacin cewa gwamnati tana da dukkan karfi da dama ta ganin bayan wadannan miyagun,” inji shi.
Buhari ya kuma jinjinawa Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle kan irin kokarin da yake yi wajen yaki da ’yan bindiga sannan ya yi alkawarin ci gaba da taimaka masa don ganin an sami dauwamammen zaman lafiya.
Da yake mayar da jawabi, Gwamna Matawalle shima jinjinawa Buharin ya yi da irin damuwar da Gwamnatin Tarayya ta nuna kan lamarin, yana mai cewa nan bada jimawa ba za a kubutar da daliban na Jangebe.
“Na gamsu kwarai da irin rawar da Shugaban Kasa ke takawa wajen yaki da kowanne irin nau’i na aikata laifi, kuma ina kiransa da ya kara kaimi a kan haka,” inji Gwamnan.
Sauran wakilan dake cikin tawagar ta Gwamnatin Tarayyar sun hada da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, Ministar Jinkai, Hajiya Sadiya Umar-Farouk da kuma Ministar Harkokin Mata, Misis Pauline Tallen.
Sama da dalibai 300 ne dai ’yan bindiga suka sace ranar Juma’a bayan sun kai hari Makarantar Sakandiren ’Yan Mata dake Jangebe a Karamar Hukumar Talata-Mafara.