Fitaccen masanin harkokin shari’a da tsarin mulkin kasar nan, Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu ya ce, duk tsawon lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai shafe wajen neman magani ba zai taba sanyawa ya rasa kujerar shugabancin kasar nan ba, domin kafin ya tafi sai da ya mika ragamar mulkin kasar ga Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
Farfesa Yadudu ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya game da masu kiraye-kirayen Shugaba Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulki, tunda Shugaban Kasar ya cika kwana 90 a wajen neman magani .
Farfesa Auwalu Yadudu ya ce “Kullum ya kamata jama’a su san cewa ana yin aiki da doka ce da kuma abin da kundin tsarin mulki ya tanada, ba tunanin wadansu mutane ba.”
Farfesan ya ce ba kamar lokacin mulkin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ba, wanda a wancan lokaci tafiyarsa ta haifar da rudani na rashin takaimeman Shugaba. “Idan za mu iya tunawa lokacin da marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa ya tafi neman magani a kasar Saudiyya ya tafi ba tare da ya bayar da riko ga Mataimakinsa Goodluck Jonathan ba. Hakan ya jawo aka yi ta tababa a kan lamarin shugabancin kasar nan. Daga baya aka bai wa Mataimakin nasa rikon shugabancin wanda kuma ya ci gaba da rikewa har zuwa lokacin da rai ya yi halinsa, inda shi Mataimakin nasa ya ci gaba da mulki a matsayin cikakken Shugaban Kasa.”
A cewar Farfesa Yadudu duk da dai an yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima amma dokar ba za ta yi aiki a kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, sakamakon yin aiki da doka da ya yi tun farko, “Bayan wannan lokaci ne saboda sabanin da aka samu na rashin bayar da mulki da Shugaban ’Yaraduwa ya yi, sai aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan gyara cewa duk wani Shugaba idan ya yi kwanaki 30 ba ya kan kujerarsa za a ba Mataimakinsa riko, idan kuma ya yi kwanaki 90, to za a ba Mataimakin rikon kujerarsa gaba daya. Sai dai wannan gyara da aka yi ba ta da nasaba da halin da Shugaban Kasa Buhari yake ciki, saboda shi ya yi aiki da doka, ya yi abin da ya dace, domin ya bayar da rikon kujerarsa ga Mataimakinsa. Duk wani abu na doka ya bi shi sau-da-kafa, domin lokacin da zai yi tafiya ta farko ya rubuta wa Majalisar Dokoki takarda cewa zai tafi hutu ko wani abu da ya yi kama da haka, lokacin da ya dawo ya sake rubuta mata takarda. Haka ma a yanzu da ya sake tafiya a karo na biyu ya sake rubuta mata takarda. Wannan gyara zai yi aiki ne kawai a kan shugaban da bai bayar da mulki don kansa ba, shi ne za a iya yi amsa wannan karfa-karfa,” inji shi.
Farfesa Yadudu ya bayyana cewa wannan gyara da aka yi wa tsarin mulkin ba zai aiki a kan Shugaba Buhari ba, saboda dokar ba ta kayyade iya lokacin da mutum zai bayar da rikon kwarya ba. Misali ba a bayyana kwana 90 ko shekara daya mutum zai iya bayarwa ba, da za a ce idan ya wuce haka mulkinsa zai salwanta ba. “Abin da muka sani shi ne an bar abin a bude har zuwa lokacin da mutum ya samu lafiya ya dawo bakin aiki. A cikin kundin tsarin mulki babu inda aka ce ga iyakar kwanakin da (Shugaban Kasa) zai iya bayarwa na rikon kwarya. Abin da muka sani shi ne kundin tsarin mulki ba zai yi aiki a kansa ba, Shugaban Kasa ya sauke nauyin da ke kansa ya yi abin da ya dace. Kamata ma ya yi a yaba masa duk da cewa bai bayyana tsawon lokacin da zai kwashe a can ba, amma ya mika ragamar mulkin kasar ga Mataimakinsa,” inji Yududu.
Da Aminiya ta nemi sanin ire-iren abubuwan da Shugaba zai yi ya rasa kujerarsa, Farfesa Yadudu ya ce a lokuta hudu kowane Shugaban Kasa zai iya rasa kujerarsa. “Shugaba zai iya rasa kujerarsa idan ya ajiye mulki a karan-kansa ko kuma idan an same shi da wasu laifuffuka an tsige shi, ko kuma a kafa masa wani kwamitin kwararun likitoci da za su iya bincikar lafiyarsa su tabbatar da gamsuwarsu cewa rashin lafiyar da yake yi ba zai iya shugabanci ba, kuma za su kai rahotonsu ga majalisa. Idan aka samu kashi biyu bisa uku na ’yan majalisa suka amince da hakan shi ke nan sai a mika wa Mataimakinsa shugabancin. Ko kuma idan ya rasu shi ke nan magana ta kare, don dama ba ya nan ballantana a yi wata cece-ku-ce a kai,” inji shi.
Farfesa Yadudu ya yi kira ga jama’a su zama masu iya bakinsu a kan wasu abubuwa sannan ya kamata su san cewa duk mai rai zai iya yin rashin lafiya a kowane lokaci haka idan Allah Ya ba shi lafiya zai iya samun sauki ya zama kamar bai taba yin rashin lafiya ba. “Ni a ganina kamata ya yi a yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya, maimakon a zauna ana yi masa kwarmato domin ya yi duk abin da kundin tsarin mulki ya tanada a kan hakan,” inji Farfesa Yadudu.