Hajiya Dada, mahaifiyar shugaban ƙasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adua ita ce matar da samun irin ta sai an tona dubunnai kafin a samu guda ɗaya da ƙyar.
Dada, wadda sunanta na asali Fatima, ita ce matar da Allah Ya yi wa baiwar haihuwar ’ya’yan da suka taɓa zama shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamna, sanata da minista a lokacin rayuwarta.
Sannan ita ce matar tsohon ministan Najeriya kuma Matawallen Kastina, Alhaji Musa Yar’Adua.
Ta rayu har sai da ta binne biyu daga cikinsu, har da shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua a watan Mayun shekarar 2010, a lokacin yana kan mulki daga 2007-2010.
Kafin nan, a watan Dimaban 1992, ta shaida rasuwar wansa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa na mulkin sojan Obasanjo daga 1979-1982, wato Janar Shehu Musa Yar’Adua.
Dattijuwar, wadda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Litinin 2 ga watan Satumba, 2024, ta rasu tana da shekaru 100 a duniya.
’Yan uwa da abokan arziki sun shaidi Hajiya Dada da kasance dattituwa mai yawan azumi, wadda azumin ranakun nafila na Litinin da Alhamis ba sa wuce ta, duk kuwa da yawan shekarunta.
Hakazalika azumin tsofaffi, daga farkonsa har zuwa karshe, azumtar sa take yi.
Manyan ’yan siyasar Najeriya suna yawan kai wa Hajiya Dada Fatima ziyara a duk lokacin da suka je Katsina, musamman a kakar zaɓe, domin nuna girmamawa a gare ta.
Babban dalilin ’yan siyasan na yin haka, ya haɗa da yadda al’umma suke ɗaukar mahaifiyar ta Yar’Adua da daraja, musamman ma kasancewarta mahaifiyar Shehu da Umarum, manyan ’yan siyasa da ake gani da mutuncim har bayan rayuwarsu.
Daga cikin manyan ’yan siyasan da suka ziyarce ta a ’yan shekarun nan akwai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a lokacin da yake takarar shugaban ƙasa.
Hakazalika tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, tsohon shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki.
Kazalika tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jamiyyar LP, Peter Obi, tsohon Gwamna Emmanuel Udom da Nyesom Wike.
Marigayiya Hajiya Dada ta rasu ta bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Sanatan Katsina ta Tsakiya mai ci, Abdulazeez Yar’Adua.