Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a jihar Gombe ta raba wa malaman ta dabura domin gudanar da aikin da’awa a yankunan karkara.
Shugaban kungiyar a jihar, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya jagoranci raba baburan ga wasu daga cikin malaman domin saukake musu aikin da’awa a yankunan jihar.
Injiniya Salisu Gombe ya ce manufar kungiyar ita ne na isar da sakon Allah ga bayinSa da suke lungu-lungu a sassan jihar ta Gombe.
Ya kuma bayyana cewa wani bawan Allah ne ya saya kungiyar baburan domin raba su ga masu aikin da’awa.
Da yake tsokaci kan rabon baburan, Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar, Sheikh Abubakar Abdullahi Lamido yace yana cike da farin ciki kan wannan abun alkhairi.
Sannan ya yi addu’a da fatan alheri ga wanda ya sanya dukiyarsa waien sayen baburan domin ciyar da addinin Allah gaba
Baburan, an raba su ne ga rassan kungiyar inda aka bai wa reshen JIBWIS na Jalingo Kamo da ke Karamar Hukumar Kaltungo, sai aka bai wa Malam Usman Manga Kumo da Malam Muhammad Rabiu.
Daga bisani Babban Daraktan Agaji na Jiha, Alhaji Maigari Usman Malala ya yi godiya tare da kira gare su da su kara kaimi ga aikin isar da sakon Allah, sannan ya sake yin kira ga al’umma da su sanya kungiyar cikin addu’a saboda wadanda suke yi mata zagon kasa.