✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da yaran Kudu aka sace zuwa Arewa da yanzu kasar nan na dumi –  Dansudu

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar ’Yan Arewa kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar Ci gaban Matasan Arewa Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu,ya ce, an dade ana satar ’ya’yan jama’a daga…

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar ’Yan Arewa kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar Ci gaban Matasan Arewa Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu,ya ce, an dade ana satar ’ya’yan jama’a daga Arewa ana kai su Kudu maso Gabas ko Kudu maso Kudu inda ana sauya masu kabila da addini da kuma al’adunsu.

Alhaji Ado Dansudu wanda kuma mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Leags, inda ya ce a karshen shekara aka fi samun bacewar yara a Arewa a wannan lokaci ne kabilun wannan yanki da ke zaune a Arewa ke zuwa gida yin bukukuwa. “A baya ana alakanta yawan batan yara a wannan lokaci na karshen shekara da miyagu ’ya’yan kungiyar asiri, a wancan lokaci ba a fargaba, ba a da masaniya cewa ana sace yaran ne a kai su Kudu a mayar da su ’ya’yan can, shi ya sa sau tari in k aga wani mutumin Kudu ka yi masa kallon tsanaki za ka gane asalinsa dan Arewa ne,” inji shi.

Ado Dansudu, ya ce da yaran Kudancin kasar nan aka sata a kai Arewa aka sauya musu suna da  addini da yanzu al’ummar yankin sun yi ta kwarmato har sai Gwamnatin Tarayya ta shiga lamarin, “Amma da yake yaran da abin ya shafa ’yan Arewa ne Musulmi babu wanda ya damu, da ’yan Kudu lamarin ya shafa da sun yi ta kwarmato a jaridu har sai gwamnati ta shiga lamarin, idan ka lura a baya wani dan Arewa ya shirya yin aure da wata ’yar kabilar Ibo a fadar Mai martaba Sarkin Bidda aka daura auren amma sai da ’yan uwanta suka yi ruwa suka yi tsaki suka kwace yarinyar. Kazalika kowa yana sane da labarin Yunusa Yellow, wanda suka yi soyayya da wata yarinya a Jihar Bayelsa ta bi shi har gida Arewa suka yi aure amma sai mutanensu suka yi ta jan maganar inda a halin da ake ciki wannan bawan Allah yana can Jihar Bayelsa a tsare a gidan yari mutanenmu na Arewa sun kasa yin komai a ceci rayuwarsa. Ya ce “Yanzu ma wadannan kananan yara da ba su san komai ba, an sace su an sauya musu suna da al’ada dama maganar addini yaro kan taso ne da abin da ya ga ana yi a gidan da yake. Tabbas ya kamata a bi diddigin wannan lamari don kwatar musu ’yancin su, sannan a binciko ragowar yaran da ke cikin irin wannan hali, sannan lallai ne Gwamnatin Tarayya ta fito ta ce wani abu a kan wannan babban al’amari, ba abu ne da za ta yi gum da bakinta ba.”

Ya ce, dole ne ‘yan Arewa su rika sanya ido sosai akan ’ya’yansu  gudun shiga irin wannan hali, domin akwai iyaye da dama da ba su san inda ’ya’yansu ke kwana ba, Allah wadansu na gararanba a tituna da sunan bara, don haka wajibi ne a dauki matakan kiyaye aukuwar haka a nan gaba.