✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da wuya in gama kwallo a kulob din Madrid – Ronaldo

Shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen, Cristiano Ronaldo a wata tattaunawa da ya yi da wata Mujallar da ake wallafawa a Jamus mai…

Shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen, Cristiano Ronaldo a wata tattaunawa da ya yi da wata Mujallar da ake wallafawa a Jamus mai suna “Kicker” ya ce har yanzu bai yanke shawarar ko zai gama kwallonsa a kulob din Madrid ba ko a’a.

A tambayar da aka yi masa na cewa “a ina yake jin zai kammala kwallonsa?” sai ya amsa da cewa “in kana nufin in canza sheka ne zuwa wani kulob, to ina da niyyar yin haka”. Sai dai bai fadi kulob din da yake niyyar komawa ba ko kuma lokacin da yake niyyar canza shekar.
“A halin yanzu dai ni dan kwallon Madrid ne kuma zan cigaba da yin kokari don ganin na taimakawa kulob din wajen samun nasara a duk wasanninta sai dai ban san abin da zai iya faruwa nan gaba ba, Allah ne kadai Ya san ko zan gama kwallona a nan ko kuma a wani wuri daban”, inji shi.
Ronaldo ya kara da cewa, “abu daya ne zan iya tabbatarwa a halin yanzu, zan cigaba da yin kokari a kulob din Madrid sannan zan rubanya kokarin da nake yi wa kasar haihuwata Fotugal”.
Tun a watannin baya ne dai aka rika baza jita-jitar Ronaldo zai canza sheka. Wasu sun yi hasashen zai koma tsohon kulob dinsa na Manchester United da ke Ingila ne yayin da wasu ke ganin kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa zai koma. Koma dai mene ne lokaci ne kurum zai tabbatar da haka.
Sai dai a shekaranjiya Laraba shugaban kulob din Madrid ya ce zai zauna da Ronaldo don su tattauna matsalar da ke damunsa musamman na furucin da ya y na cewa da wuya ya gama kwallonsa a Madrid.