Dan kasar Chinan nan da ake zargi da kisan tsohuwar budurwarsa, Ummukulsum Sani Buhari, wacce aka fi sani da Ummita, Frank Geng Quarong, ya amsa cewa shi da kansa ya yi amfani da wuka wajen kashe ta
Ya bayyana hakan ne a Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 17 da ke zaman ta a Miller Road karkashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, yayin da ta ci gaba da sauraran shari’ar ranar Laraba.
- Hanyoyi 5 da azumi ke inganta lafiyar dan Adam
- Matana da ’ya’yana ba za su shiga gwamnatina ba — Abba Gida-Gida
A zaman kotun na Laraba, lauyar Gwamnatin Jihar Kano, Barista A’isha Mahmud, ta yi wa Frang Geng Quarong tambayoyi a kan zargin da ake yi masa, inda ya shaida wa kotun cewa ya zo Najeriya ne a shekara ta 2019, kuma yana aiki da kamfanin BBY Textile wanda yake biyansa Naira miliyan daya da rabi a matsayin albashi duk wata.
Frank Geng ya kara da cewa bayan ga hakan kuma, yana gudanar da wasu sana’o’i na kashin kansa.
Aminiya ta rawaito cewa Frank ya shaida wa kotun cewa ya kashe wa Ummita sama da Naira miliyan 60 a lokacin da suke soyayya.
Wanda ake zargin ya tabbatar da cewa shi da kansa ya yi amfani da wuka ya caka wa marigayiyar wuka wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarta.
Lauyan wanda ake zargi, Barista Muhammad Balarabe Dan-Azumi ya shaida wa kotun cewa za su gabatar da wata yarinya a matsayin shaidarsu ta karshe a zama na gaba.
Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya sanya gobe Alhamis 30 ga watan Maris 2023 domin ci gaba da sauraran shari’ar