Rahotanni daga Fadar Alaafin na Oyo sun tabbatar cewa a lokacin Sallar La’asar za a yi Sallar Jana’izar Oba Lamidi Adeyemi III ranar Asabar, bayan rasuwar ranar Juma’a da dare.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ambato wata majiya mai tushe a fadar tana cewa tuni shirye-shiye suka kankama domin gudanar da Sallar Jana’izar da kuma binne basaraken a makabartar sarakuna da ke Baara.
“Ba shi kadai za a binne a Baara, a nan ake binne duk wani Alaafin; can sarakuna da ke kan mulki suke zuwa a duk lokacin da suke ganawa da kuma neman mafita daga magabatan da aka binne,” inji majiyar.
Kawo yanzu dai daya daga cikin manyan ’ya’yan sarki a Masarautar Oyo, Bishop Ayo Ladigbolu, yana ganawar sirri da ’ya’yan mamacin game da tsare-tsaren jana’izar da kuma yadda makokin mahaifin nasu zai kasance.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ya rawaito cewa an shiga zaman ne bayan babban dan marigayin, Babatunde Adeyemi, ya isa fadar.
Yunkurin jin ta bakin iyalan mamacin ya ci tura, kasancewar a cewarsu babu wata sanarwa a hukumance da aka fitar da ke bayyana rasuwar tasa.
To sai dai a ganwarsa da kamfanin dillancin labaran, kakakin marigiyain, Durojaiye, ya tabbatar da rasuwar uban gidan nasa.
Masu rike da sarautun gargajiya da dama na bayyana kaduwa kan lamarin tare da ci gaba da jiran sauran bayanai kan rasuwar.