Matashin nan mai shekara 33 kuma dan gwagwarmayar da ya lashe zaben kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar Gada/Goronyo a Jihar Sakkwato, Bashir Usman Gorau, ya ce noma ya yi ya tara kudin kamfe.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana sunan Bashir na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da karshen mako da kuri’a 29,679.
- Yau INEC za ta ba wa Fintiri takardar shaidar cin zabe
- Mai PoS ya shiga hannu kan kashe N280m da aka tura masa bisa kuskure
Ya dai doke Musa Sarkin Adar ne na jam’iyyar APC wanda ke neman sake komawa kujerar a karo na biyar, wanda ya samu kuri’a 25,549.
A tattaunawarsa da shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust, zababben dan majalisar ya ce shi daga maigidansa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ba sa yakin neman zabe da kudin gwamnati.
Ya ce, “Ba za ka zo ka ce da Tambuwal ya yi amfani da baitil-mali wajen kamfe ba, idan ka fada masa cewa zai yi idan aka je Lahira kai za ka amsa min tambayoyina?
“Kamar ni alal misali, na biya kudaden kamfe dina ne da noman da nake yi da kuma kasuwanci. Kowa ya san ni manomi ne. Duk wanda ka tambaya ya san daga wata 14 zuwa yanzu ba na ofis,” in ji shi.
Bashir dai kafin cin zaben nasa shi ne Kwamishinan ci Gaban Matasa da Wasanni na Jihar ta Sakkwato, kuma yi takara ne a PDP.
Nasarar da ya samu kuma ta kara yawan matasan da suka yi ba-zata wajen lashe zabuka a zaben na 2023.