✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da ‘kudin haram’ aka sayi gidan da Buhari ya ziyarci Tinubu

A 2016 Gwamnatin Buhari ta bukaci kotu ta kwato mata gidan

Takardun Pandora sun bankado wata badakala da ta shafi gidan da jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi zaman jinya, inda kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarce shi.

Wani rahoto da kafar yada labarai ta Premium Times ta bayar ya nuna cewa a 2016 Gwamnatin Buhari ta samo umarnin kotu a kan a hana saye ko sayar da gidan kafin mamallakinsa ya sayar wa wani kamfanin kasar waje mallakar Gwamna Gboyega Oyetola na Jihar Osun.

“A shekarar 2016 Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta nemi umarni daga Babbar Kotun Tarayya da ke Legas a kan kwace wani jerin kadarori mallakar [Kola] Aluko da [Jide] Omokore wadanda aka kiyasta farashinsu ya kai Fam biliyan 1.8”, inji rahoton.

Premium Times kadai ce kafar yada labaran Najeriya da ta shiga binciken da ya bankado wasu miliyoyin takardu da ke dauke da bayanan yadda wasu fitattun mawadata da masu mulki na duniya ke boye kudaden haram.

Gidan mai fadin murabba’in kafa 6,975 a Titin Grove End da ke unguwar masu hannu da shuni ta Westmenster a birnin Landan yake.

Gida na kasaita

Wata takardar talla da shahararren kamfanin dillancin kadarori na Birtaniya, Savills, ya fitar ta nuna cewa gidan na da gine-gine biyu.

Ranar 12 ga Agusta Buhari ya ziyarci Tinubu

Gini na farko na da dakuna biyar da zauren karbar baki da dakin karatu da babban dakin kwana – mai dakin ajiye tufafi da bandaki – da sinima.

Daya ginin kuma flat ne mai daki biyu da bandaki da dakin girki wadanda aka gina a saman garejin mota mai fadi.

Gidan na kuma da lambu a baya.

Ayar tambaya

“Wasu takardu da aka samu a hukumar rajistar kadarori ta Birtaniya sun nuna cewa a watan Yulin 2013, wani kamfanin dodorido da aka kafa a Tsibiran Virgin mai suna Zavlil Holdings ya sayi kadarar a kan kudi Fam miliyan 11.95”, a cewar rahoton na Premium Times.

“Takardun sun nuna cewa Kolawole Aluko, wanda hukumomin tsaro a Najeriya da Amurka ke nema ruwa a jallo bisa zargin halalta kudin haram, shi ne ya mallaki kamfanin Zavlil Holdings Limited.

“An tuhumi Kola Aluko da abokin huldarsa, Jide Omokore, a Amurka da Najeriya bisa zargin almundahana da halalta  kudin haram da hadin gwiwar tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Allison Madueke”.

Rahoton ya kuma ce jim kadan bayan kotu ta bayar da umarnin hana saye ko sayar da gidan ne Aluko ya sayar da shi a kan kudi Fam miliyan 9 ga Aranda Overseas Corporation, wani kamfanin dodorido da wasu yaran Tinubu biyu wadanda ya fi yarda da su suka kafa a Tsibiran Virgin.

Wadannan yara na Tinubu su ne Oyetola, wanda ya taba shugabantar Ayarin Kamfanonin Paragon, da Elusanmi Eludoyin, wanda ya gaje shi.

“Yadda aka karyar da farashin gidan ya diga ayar tambaya a kan ko Mista Aluko ya matsu ne ya sayar da shi duk da umarnin kotu da ya haramta yin hakan”, inji rahoton.

‘Tabbas, gidan Buhari ya je…’

A bukatar da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kotu, ba a rubuta lambar gidan ba, amma binciken da Premium Times ta ce ta gudanar a Najeriya da Birtaniya, da ma nazari mai zurfi a kan hotunan da aka wallafa na ziyarce-ziyarcen da ’yan siyasa suka kai wa Tinubu, sun tabbatar da cewa gidan da jagoran na APC ya yi jinya ne Gwamnatin Najeriya ta nemi a kwace.

“Bugu da kari”, inji Premium Times, “mun iya tantance cewa a wannan gidan ne dai Mista Tinubu ya karbi bakuncin Shugaba Buhari, wanda ya ziyarce shi ranar 12 ga watan Agusta, da sauran ’yan siyasar da suka je gaishe shi.

“Wakilanmu sun yi Nazari na tsanaki a kan wasu daga cikin hotunan wadannan ziyarce-ziyarce, sannan wasu majiyoyi na kusa da Mista Tinubu sun tabbatar da cewa a gidan ne ya karbi bakuncin wadanda suka ziyarce shi, ciki har da Shugaba Buhari.

“Musamman, biyu daga cikin hotunan ziyarar Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun sun taimaka sosai wajen fito da lamarin fili”, inji rahoton.

Premium Times ta ce ta tuntubi mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, game da abin da bincikenta ya nuna, amma ya yi alkawarin mayar da martini a cikin sa’o’i 24.

Sai dai kuma har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton ba a ji daga gare shi ba.

A cewar kafar ta Premium Times, shi ma kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu, da aka tuntube shi ya yi alkawarin mayar da martini amma shiru kake ji, kamar an shuka dusa.