✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da karfin bindiga aka kwace motocina – Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe Mista Charles Ya’u Iliya, ya ce ba shi da kansa ya mika wa Kwamitin Karbo Kadarori da Gwamnatin Jihar Gombe,…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe Mista Charles Ya’u Iliya, ya ce ba shi da kansa ya mika wa Kwamitin Karbo Kadarori da Gwamnatin Jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya kafa motocinsa na hawa ba, kamar yadda Shugaban Kwamitin ya fada ba, inda ya ce jami’an tsaro ne da bindigogi suka kewaye gidansa, sannan ya mika musu ba a son ransa ba.

Mista Charles Iliya, ya ce da karfin bindiga aka shiga gidansa aka ce ya kawo motocin da aka yi masa kudinsu ya biya kamar yadda ake yi wa kowane jami’in gwamnati a matsayin Mataimakin Gwamna.

“’Yan sanda ne suka je gidana bisa jagorancin wani babban jami’insu suka shiga har cikin babban dakina wadansu kuma suna kofar gida a tsaye wadansu a harabar gidan, mutum hudu har da shi babban nasu a cikin gidana kowanne da bindiga suka tsaya a kaina suka ce min  an turo su ne in ba su motocina,” inji Charles Iliya.

Ya ce ya nuna musu takardun shaida na kudin motocin da ya biya, amma suka ce masa sam sai ya bayar da su domin su aikin kwamiti suke yi, inda ya ce, “dole na ba su, saboda babu yadda na iya domin sun ce kwamiti ne ya sa su kuma aikin Gwamna ne.”

Ya kara da cewa sun  nuna masa takardar shaida ta bincike (search warrant) da ta ba su dama su binciki gidansa saboda wadannan motoci, shi ma ya ce ya nuna musu nasa na mallakar motocin amma suka ki yarda.

Tsohon Mataimakin Gwamnan ya ce bayan sun ga motocin sun bincika sun ga lafiyar su sai suka tattara su suka tafi da su. “Motocin uku ne Ledus Jeep daya da Prado Jeep biyu, kuma tunda suka tafi da su ba su kuma dawo da su, ba su dawo min da kudina ba,” inji shi.

Daga nan sai ya bayyana cewa jita-jita ce wadansu mutane  ke yadawa cewa wadansu ’ya’yan jami’iyyarsu ta PDP sun ba shi motoci daga jin faruwar hakan, a cewarsa bai yi waya da kowa ba a cikin jiga-jigan na PDP har zuwa yanzu kan lamarin.