✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da hadin bakin sarakuna ake wa tsaro zagon-kasa —Sarkin Bassa-Nge

A hukunta duk wanda aka kama ya aikata haka don ya zama darasi ga saura

Sarkin Masarautar Bassa-Nge a Jihar Kogi, Birgediya Abu Ali (mai murabus), ya bayyana takaicinsa kan yadda ake hada baki da wasu sarakuna da shugabannin addinin wajen yi wa fannin tsaro zagon-ƙasa a Najeriya.

Basaraken ya bayyana hakan ne a hirarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

“Abin bakin ciki ne sarki ko shugaban addini ya zama da shi ake hada baki wajen kassara tsaro, wanda hakan kan shafi zaman lafiya da ci gaban kasa.

“Ta bangarena, babu yadda za a yi wani bata-gari ya shigo yankina ba tare da na sani ba.

“Don haka duk wani sarki da yake barin miyagu na gudanar da harkokinsu a yankinsa, hakan alama ce ta hadin baki wanda tilas hukumomi su dauki matakin magancewa,” in ji shi.

Ya kara da cewa dole ne a dauki kwakkwaran mataki wajen hukunta duk wanda aka samu da aikata haka don ya zama izina ga saura.

Ya ce kamata ya yi sarki ko shugaba na addini ya zama mai ba da gudunmawa wajen yaki da matsalar tsaro ta hanyar fallasa duk wasu ayyukan da bai yarda da su ba a yankinsa maimakon bai wa miyagu mafaka.

(NAN)