Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta sanar da cewa za ta ci gaba da yajin aikin da ta dakatar a Jihar Kaduna.
Shugaban NLC na Kasa, Kwamaret Ayuba Wabba, ya ce sun dauki matakin ne saboda Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya gaza cika yarjejeniyar da aka kulla.
- APC za ta samu matsala idan Buhari ya sauka mulki —Lawan
- IPMAN ta dakatar da kai mai zuwa Abuja da wasu jihohi
Da yake sanar da manema labarai hakan bayan taron gaggawa da kungiyar a Abuja, ranar Talata, Wabba ya ce daga cikin kokarin da suka yi, sun aike da wasika zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige, amma hakan ya gaza samar da wani kyakkyawan sakamako.
Ci gaba da yajin aikin da NLC ta dakatar na iya zama na gama-gari a fadin Najeriya, idan har kungiyar ta tsaya kan bakarta, yadda ta sanar a lokacin dakatar da shi a makonnin baya.
Tsugune ba ta kare ba
Matakin na NLC na zuwa ne bayan a ranar Alhamis Gwamna El-Rufai ya sanar cewa gwamnatinsa na kokarin bincikowa da zakulo ma’aikatan Jihar da suka shiga yajin aikin da kungiyar ta gudanar a kwanakin baya.
Ya sanar cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an hukunta ma’aikatan da shugabannin kungiyan saboda abin da ya kira durkusar da harkoki a Jihar tasa.
Yajin aikin Kaduna
Yajin aikin NLC a Jihar ya samo asali ne daga yunkurin El-Rufai na sallamar dubban ma’aikata bisa hujjar cewa kudin da gwamnatin jihar ke kashewa wurin albashinsu ya haura kashi 80% na abin da take samowa daga Gwamnatin Tarayya.
A kan hakan ne ya umarci daukacin kananan hukumomin jihar da su rage yawan ma’aikatansu zuwa mutum 50 a kowacce daga cikinsu.
Duk da tir din da aka yi da matakin tare da neman ya dakatar da yunkurin, gwamnan ya sanar cewa babu gudu, babu ja da baya.
A bisa haka ne kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi tare da gudanar da zanga-zangar lumana a Jihar Kaduna, har sai da Gwamnatin Tarayya ta sanya baki NLC ta janye, aka hau teburin sulhu.
A lokacin da take janye jayin aikin, NLC ta ce muddin ba ta samu biyan bukata ba, to za ta koma yajin aikin, kuma zai iya zama na gama-gari a fadin Najeirya.