✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da buga bulo da hannu na fara kasuwanci – Alhaji Nasiru Ahli

Alhaji Nasiru Ahli Isma’il fitaccen dan kasuwa ne da sunansa ya yi tambari a Najeriya, ya shaida wa Aminiya cewa ya fara harkokin kasuwancinsa ne…

Alhaji Nasiru Ahli Isma’il fitaccen dan kasuwa ne da sunansa ya yi tambari a Najeriya, ya shaida wa Aminiya cewa ya fara harkokin kasuwancinsa ne da buga bulo da hannnu a karshe ya shiga harkar dab’i. Shi ne mamallakin Kamfanin Mainasara and Sons Group of Companies. A  wannan tattaunawa, dan kasuwar mai kimanin shekara 98 ya shaida wa Aminiya yadda ya fara kasuwancinsa da kuma yadda yakin Maitatsine ya kare:

 

Kasancewarka fitaccen dan kasuwa, yaya aka yi ka fara kasuwancinka?

Kafin in fara kasuwancin bulo, ina harkar cinikin filaye da abin da ya danganci haka domin ina bayar da hayar gidaje ina kuma harkar gwanjon kayayyaki. Har yanzu ina da lasisin gwanjo, wanda na samu daga Hukuma. Sai ga shi cikin kankanin lokaci na yi fice a cikin harkar bulo saboda na jajirce a kan harkar. Da farko muna yin bulo din da hannu, sai dai ba na jin dadin aikin a haka. To lokacin Gwamnan Jihar Kano Audu Bako, Aminu Dantata shi ne Kwamishinan Kasuwanci da Masanan’antu sai na nemi bashin Fam din Ingila 1,000 don in sayi injin yin bulo. Aka amince min, sai aka yi sa’a Aminu Dantata ya kawo wasu injunansa da zai yi aikin ginin filin jiragen sama na Zariya kuma injiniyoyinsa sun gaya masa cewa wannan inji zai ba su matsala saboda zai rika shan man fetur sosai.

Da na ji haka sai na je na nemi ya ba ni  injin kuma ya karbi takardar bashin, inda ya karbi kudin a madadina. Cikin ikon Allah kasuwancin bulo ya karbe ni har wata rana na gayyaci Aminu Dantata da Umar Gumel Magajin Kazaure da Madaki Gauyama na Hadeja, inda muka bude kamfanin buga bulo na Nasara a Sabon Gari. Malam Aminu Kano shi ya shawarce ni in yi wa kamfanina rajista da sunan Malam Mainasara amma ni sai na ji na fi son Mainasara kawai. Don haka na yi rajista da Mainasara and Sons.

Da muka fara harkar buga bulo muna karbar kasa da siminti bashi, sai mun sayar sannan mu biya har zuwa lokacin da muka samu injinmu daga Aminu Dantata. Muna yin kasuwancin ba ni gishiri in ba ka manda da Alhaji Sani Zango na Kofar Mata, inda muke karbar kasa a wajensa shi kuma ya karbi bulo daga wurinmu.

A wancan lokaci muka kulla alaka da Gwamna Audu Bako, domin yakan baro ofishinsa ya kawo min ziyara ofishina da ke kan titin Club Road. Wata rana ya zo ofishina ya ga injiniyoyi suna sanya mana inji, don haka sai ya hada ni da wani surukinsa dan gidan Saleh Jambo, wanda muka je kasar Italiya tare shi muka sayo wani injin da muka rika aikin bulo da shi.

Ta yaya za ka kwatanta tasirin da injin da kuka sayo a kasar Italiya ko ya bunkasa harkar kasuwancin bulo dinka?

Lokacin da muka dawo daga kasar Italiya, wannan inji da muka sayo ya bunkasa kasuwancina kwarai da gaske, domin mukan yi bulo guda 10 zuwa 20 a lokaci guda. A wancan lokaci sai da ta kai babu wani bulo da ake ji da shi a Kano kamar Mainasara sai kuma wani bulo mai suna Mahmun sai kuma na wani Ibo ne amma ba zan iya tuna sunansa yanzu ba.

Lokacin da aka yi Yakin Basasa na kula da gidajen Ibo sama da 20 a cikin Sabon Gari. Idan lokaci ya yi zan karbi kudin hayarsu in dauki nawa kason, in ba wakilinsu nasu kudin. Haka muka rika yi har zuwa lokacin da abubuwa suka daidaita suka dawo Kano. Wadanda suke harkar dab’i daga cikinsu suka dawo suka ci gaba da ayyukansu.

Yaya aka yi ka fara harkar dab’i?

Wadansu daga cikin Ibo da suka gudu suka bar Kano lokacin Yakin Basasa suka nemi in kula musu da shagunansu da suke harkar dab’i, sai wani wanda ke da wani kamfanin dab’i daga cikinsu bai dawo ba, don haka sai na rika amfani da kamfaninsa ina biyan kudin haya Naira 20. To lokacin ban iya harkar ba sai Audu Bichi, wanda shi ne Sakataren da ke kula da dab’i na tsohon Gwamna ya nuna min yadda zan yi harkar. To kun ji yadda na shiga harkar dab’i.

Lokacin da na gane harkar tana da albarka sai na nemi bashi daga Bankin Masana’antu, inda na sayo injin din dab’i da takarda da sauran kayan aiki. A lokacin kayan aikin dab’i suna wahalar samu a Legas, domin a lokacin sai mutum ya tura kudinsa da wuri kafin ya samu. To a wancan lokacin sai na yi abokai da yawa, cikinsu har da Gwamnan Babban Bankin Najeriya na wancan lokaci, Abdulkadir Ahmed Jama’are wanda ya taimaka min har na samu takardar bashi ba tare da kwabona ba,  kuma har gwamnati ta ba ni lasisi kamar kowane mai dab’i. Aka ba ni dakin ajiya inda nake ajiye kayana bisa yarjejeniyar cewa duk mai son sayen kaya idan ya zo zai biya su kudin, shi kuma ya karbi kayansa har zuwa lokacin da suka sayar da kayan daidai da bashina. Abin da ya yi saura kuma shi ne ribata. A wancan lokaci ana karancin takarda a Legas, don haka sai in ciko jirage uku da takardu daga kasar waje. Nan da nan sai abokan ciniki suka rika barkowa don sayen takardu daga wurina. Duk da ina sayarwa amma ina amfani da wasu don yin dab’ina. To kun ji yadda aka yi na fara shigo da takarda daga kasar waje.

Wannan kudi da na karba ba su wuce Naira dubu 500 ba, su ne kudin da na sayi kayan aikin da na rika buga littafin rubutu na dalibai da sauran kayayyakin dab’i.

Me kake bugawa lokacin da ka fara harkar dab’i?

Na fara da buga cikakken Alkur’ani wanda na tabbatar rubutun Malam Babablle na Tudun ’Yantandu ne, wanda kuma hakkin mallakar Alhaji Sanusi Dantata ne. Na je da kaina na nemi yardarsa don buga shi, wanda kuma ya ba ni izinin yin hakan. Wannan shi ne abin da muka rika yi. Sai dai yanzu takardar da ake buga Alkur’ani da ita ta yi tsada kwarai da gaske, ba za mu iya sayenta ba. Da a ce akwai irin wannan takardar a wurinmu to da ba za mu daina buga wannan ba, kasancewar a yanzu a Jihar Kano babu irin wannan Alkur’ani na Malam Baballe.

Daga baya na fara zuwa Legas da kaina don sayen irin kayan da ake sakawa, wadanda ake shigo da su daga kasashen waje musamman ma kasar Indiya, inda kuma nake sayar da su a Kano. Daga nan kuma sai na shiga harkar gine-gine, inda na yi rajista har ma na fara samun kwangila daga gwamnati da kuma sauran manyan mutane masu zaman kansu. A lokacin na yi harka da jama’a da dama har zuwa lokacin da na rasa kudi a hannuna, lamarin da ya jawo na daina harkar gine-gine gaba daya.

A wancan lokacin Bankin Arewa yana nan haka kuma babu ’yan Arewa a cikinsa, haka kuma kan ’yan Arewar a wancan lokaci ba a waye ba, ba mu san hakkokinmu ba. Da mun san hakkinmu don ba ni kadai ba ne da wani ba zai zo ya yi mana abin da suka yi mana ba, inda suka rika matsa mana.

Ina da gida a Apapa da ke Legas wanda na saya Naira dubu 600, wani lokaci sai muka ji ana yada jita-jitar cewa za a kori duk wani dan Arewa daga Legas. Hakan ya sa na fara addu’ar Allah Ya sa na samu wanda zai sayi injina a kan farashi mai kyau. A wancan lokacin na sayi wata ma’ajiyar kaya daga Kamfanin UAC, Wani abu da kamfanin UAC ya kebanta da shi, shi ne idan ya tashi sayar da kayayyakinsa yana sayarwa ne ga ma’aikatansa da niyyar tallafa musu. Na sayi wannan sito a kan Naira dubu 600 daga hannun Akanta Janar na Kamfanin UAC na wancan lokaci. A lokacin da na ji waccan jita-jita hankalina ya tashi matuka, inda na tafi wajen Sarkin Kano wanda aboki ne ga Shugaban Kamfanin UAC na kasar nan, na gaya masa cewa akwai wani sito nawa a Appa wanda Kamfanin UAC ke son sayarwa don haka ni ma nake so in mallake shi. A nan Sarkin ya yi dariya sai ya rubuta wasika ya ba ni, na kai wa Aliyu Gusau wanda kuma abokina ne. Sai Aliyu Gusau ya kira Manajan Daraktan Kamfanin da ke kula da harkar sannan ya gaya masa cewa “Wani abokinmu ne yake son sayen wani wuri da za ku sayar. Yanzu muna jira ka aiko da mutanenku da za su yi wa wurin kima tare da shi. Sun kira sunan mutumin Ernest Shonekan da kuma wani da ake kira Aliyu Mohammed. A nan suka fito da takarda inda ya nemi in ba shi wani abu idan an gama. A take na amince inda ya kawo min takarda a kan Naira dubu 600, kuma na biya Naira dubu 300 na kuma ba wa Manajansu Naira dubu 100. Tun daga wancan lokaci na mallaki takardar. Shi ke nan kuma na mallaki wannan sito. Na kashe abin da ya kai kusan Naira dubu 600. Sai kuma na karbi hayar shagon a kan Naira miliyan biyu. Daga baya na sayar da siton a kan Naira miliyan 23. Bayan an biya ni kudina sai na fara harkar yi wa kasa kima.

Daga baya na biya rabin bashin da ake bi na na banki wanda daga baya Allah Ya taimake ni na karasa biyansu. Baya ga wannan kuma ina da wani bashin da Bankin Arewa, sai dai lokacin da Shugaba Obasanjo ya dauke Hedikwatar Bankin daga nan Arewa ya kai ta Legas wanan abu da ya yi ya janyo bankin ya lalace.

Daga baya sai na sayar da wani wurina a Abuja, inda na zo na karasa biyan bashin. Daga nan na samu natsuwa saboda babu sauran mai bi na bashi. Wurin da na sayar a Unguwar Asokoro yake, inda a yanzu kimarsa ta kai Naira biliyan daya. Da yake wata katuwar gona ce na saya na mayar da ita gidan zama. Na je Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, inda na nemi su taimaka min yadda zan tsara filin inda suka fitar da filaye kimanin 50 daga cikinta. wanda na sayar don bukatar da nake da ita.

Daga nan na samu wasu kudi a hannuna, inda na fara wannan harkar. A yanzu haka na sayar da dukan filin, a yanzu da nake magana da ku ina da wasu gidajen a wasu wuraren. Alhamdu lillah.

Lokacin da rikicin Maitatsine ya tashi kana ina?

Ina Daura lokacin da rikicin Muhmmadu Marwa ya tashi. Wannan mutumin ya yi sanadin asarar rayuka masu yawa. Allah ne kadai Ya tserar da mu, ni da dana Umar da ’yata Rabi da sauransu. Wadannan suna daga cikin mutanen da ya kwashe daga wurina. Duk da cewar ya kashe ’ya’yana biyu da wani daga cikin ma’aikatana. ’Yata ta shafe kwana  40 a gidan Maitatsine domin a can aka haife ta. Zan iya tuna lokacin da Babangida ya zo Kano don ya yaki Maitatsine sai ya aiki sojoji don su share masa hanya. Ya zo har gidana na yanzu tare da Hamza Abdullahi da Janar Halliru Akilu. Bayan Sallar La’asar mutanen nan suka gama aikinsu. Allah Ya taimake mu muka yi nasara a kansu, domin bayan gidana cike yake da konannan makamai masu guba. Wani daga cikin mutanen da muke tare da su su uku sai ya ce ba zai zauna tare da mu ba saboda ya tsorata amma sai ga shi kuma yakin ya kare a wannan lokaci.

Akwai wadansu Indiyawa da suka zo Kano suka je Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje suka nemi ganina, suna kan hanyarsu ne a Unguwar Gwauron Dutse ba su yi aune ba sai suka fara ganin mutane suna barkowa daga Mandawari zuwa Gwauron Dutse ga kuma mutanen Maitatsine suna gudu kasancewar Maitatsine ya ba su umarnin kada su yi jefa ko su doki wani. Sai daga baya Indiyawan suka samu hanya suka zo suka yi mini ta’aziyya. A wanann lokaci tuni an kashe Maitatsine din, yana ta zubar da jini, suna kokarin barin cikin gari sai ga shi ya fadi, inda kuma mabiyansa suka dauke gawarsa suka ci gaba da tafiyarsu har sai da suka kai garin Rimin Gado. A can suka zauna har suka yi masa jana’iza. Wani daga cikin manyan na kusa da shi da ake kira Turnuku shi ya gaya wa sauran mabiyan cewa Malam fa ya mutu don haka kowa ya yi ta kansa. Daga nan kowa ya gudu.

Yaya aka yi ’ya’yanka suka fada hannun Maitatsine?

Mabiyansa ne suka kama kimanin mutum 33 a lokacin suna yawo da su kamar wasu shanu. Allah ne kawai Ya tserar da su domin ba dukansu ne suka mutu ba.

A wancan lokacin rikicin kwana nawa ka yi a nan kafin ka koma can gida?

A gaskiya ba zan iya cewa ba amma na shafe wasu kwanaki kafin iyalaina su dawo su same ni a nan. Ina nan gidan har sai da aka kawo karshen komai. Matana sai suka zauna a gidajen makwabta kafin a karasa aikin ginin gidan. Zan iya tunawa lokacin da nake aikin wani sashe na gidan nan aka rika kama mabiyan Maitatsine, kasancewar akwai wata shaida a jikinsu. Wadansu a kirji, wadansu nasu a hammata da sauran wurare. A gaskiya ya kamata mu gode wa Allah, domin mun ga abin da ba mu taba tunanin faruwarsa ba.