Mazauna jihar Kaduna sun bayyana ra’ayoyinsu game da sauyin ranar dokar fita daga Asabar zuwa Alhamis, suna cewa wayon a ci ne ya sa aka kori kare daga gindin dinya.
Akasarin jama’a dai sun danganta sauyin da gwamatin jihar ta yi na mayar da ranakun fita daga Laraba da Asabar zuwa Laraba da Alhamis da cewa shiri ne domin hana sallar Idi.
Wani mazaunin layin Charanchi Road by Kerawa a Tudun Wada, Ibrahim Oso, ya ce abin da gwamnartin ke yi wa jama’ar jihar bai dace ba.
- Sallar Idi: El-Rufa’i yayi watsi da bukatar limaman Kaduna
- Yadda rufe iyakar Kaduna da Plateau ta rutsa manyan motoci
“Muna ganin an yi sauyin ne kurum domin hana mu sallar Idi; in ba haka ba me ya sa ba za a bari a fita ranar Asabar ba?
“Watau ba a son a fita idi. Allah ya shirye mu baki daya”, inji shi.
Shi ma Muhammad Siasia cewa ya yi ba a yi wa mutane adalci ba saboda ranar Juma’a ce jajibirin sallah.
“Ka ga ranar ce mutane za su fita su nemi abincin da za su yi bukukuwan salla.
“Haka kuma a ranar Asabar da ake ganin za a yi bikin sallar ya ce ba za a fita ba. Gaskiya bai mana adalci ba,” inji shi.
Ranakun sayen abinci
Shugaban Hukumar Raya Kasuwani ta Jihar Kaduna, Muhammad Hafiz Bayero, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu. ya ce daga yanzu ranar Laraba da Alhamis ne kurum aka amince mutane su fita zuwa kasuwannin unguwanni domin yin sayayyar kayan abinci.
Ya ce ba a bukatar ganin kowa a kasuwannin a ranar Asabar mai zuwa domin laifi ne a fito a bude kasuwa.
Ya shawarci jama’a su rika sanya takunkumi da yawaita wanke hanayensu.