✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cuwa-cuwa ce babbar matsalar harkar jiragen sama – Kaftin Ado

Mataimakin Babban Daraktan Kamfanin jiragen sama na Arik, Kaftin Ado Sanusi, wanda kuma tsohon Babban Daraktan Hukumar Kula da Sararin Sama ne (NAMA). A wannan…

Mataimakin Babban Daraktan Kamfanin jiragen sama na Arik, Kaftin Ado Sanusi, wanda kuma tsohon Babban Daraktan Hukumar Kula da Sararin Sama ne (NAMA). A wannan tattaunawar da Aminiya ya  yi tsokaci game da yunkurin farfado da kamfanin jiragen sama na kasa (Nigeria Airways) da ake son yi. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da niyyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta farfado da kamfanin jiragen sama na kasa wato (Nigeria Airways)?
 Kaftin Ado: Ai akwai abin la’akari a maganar da Shugaba Buhari ya yi domin ya ce za a farfado da kamfanin, amma mu mun san abin da ya suma ake farfado da shi ba wanda ya mutu murus ba. Sai dai a kafa wata sabuwar kamfanin garas. Bana cikin gwamnati balle na san yadda za a lalubo kudin da za a fara sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya. Abin da na ke ji ta kafafen yada labaru shi ne gwamnati na kokarin ganin ta inganta harkar kiwon lafiya domin asibitoci sun koma gurin tuntuba kawai. Sannan ga harkar rashin aikinyi ga matasa, samar da ilimi, tsaro da matukar rashin kudi. Ga mai nazari a yanzu maidowa ko kafa sabon kamfani ba shi ne ya fi muhimmanci ba. Amma in har akwai kudi a kasa, to sai a kafa sabon kamfani. Amma ya dace a gane mene kamfanin jiragen sama na kasa na gwamnati. Shi ne kamfanin da gwamnati ta mallaka na kanta. In kuma ba a yi haka ba, sai a sami hadakar kamfanonin jiragen sama da alamar tutan kasa. Shi wannan mai alamar tutan kasa zai iya zama na hadaka tsakanin gwamnati da ’yan kasuwa wanda ke zirga-zirga tsakanin manyan kasashen duniya a cikin yarjejeniyar fahimtar juna. Wannan ba zai ci kudi da yawa ba. Ina son in sami wannan hadaka da kuma samin tallafin gwamnatin tarayya. Ina so gwamnati ta san dalilin da ya sa kamfanin Nigeria Airways ya durkushe. Ababen sun hada da rashin iya shugabanci, rashin kudi, da cuwa-cuwa da dai sauransu. An kashe kudi da yawa a kamfanin don neman farfado da kamafanin daf da mutuwarsa, amma yin ruf da ciki ya sa hakan bai yiwuwa ba. Wannan cuwa-cuwar ita ce babbar matsalar harkan hada-hadan jiragen sama. A ganina bayan bangaren man fetur, sai na hukumomin kula da al’amuran jiragen sama. In har an dakile wannan almundahanar aka kuma sami mutanen kirki ana iya samar da kamfanin jirgin saman kasa da zai dawo da martabar Najeriya.
Aminiya: A matsayin ka na jami’i a kamfani mai zaman kansa, ko kana ganin wannan barazana ne a gareku?
 Kaftin Ado: Ba razana ba ne don muna hada-hada ne a kasuwa inda wanda ya fi karfin jari shi ya fi samin mabiya. Ai samin yawan kamfanonin jiragen sama zai kara sa gasa da inganta aiki.
 Aminiya: Shin za ka so kamfanonin jiragen saman Najeriya su dunkule?
 Kaftin Ado: Ana gamin gambizan kamfuna waje guda ne ta sayen kamfanino da kuma ta hanyar ganin dama in ra’ayi ya zama daya. Ba ana yin shi bane da karfi. Wanda suka fahimci juna suna iya dukulewa.
Aminiya: Shin kana ganin kwallayi za ta biya kudin sabulu kuwa?
 Kaftin Ado: Za ta iya cin nasara idan ka yi la’akari da yadda bankuna suka dunkule, ai a cikin fahimta suka yi haka.