✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar shawara ta hallaka mutum 115 a Katsina

Cutar Shawara da ta barke a Karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina, tayi sanadiyyar mutuwar mutum 115, kamar yadda binciken mu ya tabbatar. Mazauna…

Cutar Shawara da ta barke a Karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina, tayi sanadiyyar mutuwar mutum 115, kamar yadda binciken mu ya tabbatar.

Mazauna yankin sun bayyanawa majiyarmu cewa, mutum 115 ne suka rasa rayukansu a tsawon mako uku da barkewar cutar. Sai dai a bangaren gwamnati ta bayyana cewar mutum 18 ne kacal suka mutu.

Wani tsohon Kansila na yankin Kogari, Malam Sule Ibrahim, ya bayyana cewar cutar ta fara ne ta garin Kogari kafin daga bisani ta yadu zuwa Unguwar-Sarka, inda ya ce cutar ta hallaka mutum 115 a cikin makonni uku.

Sai dai anasa bangaren, Sakataren sashen kula da lafiya a matakin farko, Dakta Shamsu Ahmad ya ce, “An samu bullar cutar shawara, sai dai a bayanan da ke gabanmu mutum 45 ne suka kamu, yayin da mutum 18 suka rasa rayukan su, a ranar Litinin”.

Ya kara da cewa, a kwanan nan aka yi wa kimanin mutum miliyan shida allurar rigakafin kamuwa da cutar shawara a jihar.