Cutar sankarau da ta bulla a Jihar Jigawa, ta yi ajalin mutum 20, lamarin da ya haifar da fargaba ga mazauna jihar da ma hukumomin lafiya baki daya.
A sanarwar da Dokta Salisu Mu’azu, Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya ya fitar, an tabbatar da cutar a mutum 80 daga cikin 360 da ake zargin sun kamu da ita.
- Zaben 2023: Gwamnati ta bayar da umarnin rufe makarantun kimiyya da fasaha
- Mutanen da girgizar kasa ta kashe a Turkiya da Syria sun zarta dubu 36
“Muna bakin cikin tabbatar da bullar cutar sankarau a Jihar Jigawa.
“Mun tabbatar da mutum 80 sun kamu, kuma abin takaici, mutum 20 sun rasa rayukansu sakamakon wannan cuta,” in ji shi.
Dokta Mu’azu ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na daukar duk matakan da suka dace don shawo kan lamarin
“Muna aiki kafada da kafada da jami’an kiwon lafiya da kungiyoyi don tabbatar da cewa an samar da ingantattun tsare-tsare ga yankunan da abin ya shafa kuma za a samar musu da kulawar da suke bukata,” in ji shi.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), sankarau cuta ce mai tsanani da ke shafar kwayoyin halittar da ke rufe kwakwalwa da kashin baya.
Alamomin sankarau sun hada da zazzabi, ciwon kai, sarkewar wuya da kirji.
Idan ciwon ya yi tsanani, tana iya haifar da lalacewar kwakwalwa, a wasu lokutan ma ta kan kai ga mutuwar mutum.
Barkewar cutar ta haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankunan da lamarin ya shafa, kuma gwamnati na shawartar mutane da su dauki matakan kariya domin kaucewa kamuwa da cutar.
Wadannan matakan sun hada da tsafta, kamar wanke hannu akai-akai da nisantar cudanya da mutane musamman wanda suka kamu da ita, da kuma yin allurar rigakafin cutar.
“Muna kira ga kowane mutum a Jihar Jigawa da ya dauki matakin kare kansa da iyalansa daga kamuwa da cutar sankarau.
“Muna yin duk abin da za mu iya don shawo kan wannan cuta tare da tabbatar da cewa kowa ya samu kulawar da yake bukata.”
Haka kuma gwamnatin jihar ta kafa kungiyoyin bayar da agajin gaggawa da za su sa ido da kuma daukar matakan dakile yaduwar cuta.
An kuma tura karin jami’an kiwon lafiya zuwa yankunan da lamarin ya shafa domin bayar da tallafi.