Rahotanni daga Jihar Jigawa sun ce akalla 100 sun mutu sakamakon barkewar Cutar Sankarau a Jihar, kuma galibin wadanda lamarin ya shafa yara ne ’yan kasa da shekara 11.
Bayanai sun ce tun a watan da ya gabata aka samu bullar cutar a Jihar, sannan ta fi kamari ne a tsakanin Kananan Hukomin Jihar da ke iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
- Rukunin farko na maniyyata Aikin Hajji sun tashi zuwa Saudiyya
- ISWAP ce ta kai hari a cocin Ondo – Gwamnatin Tarayya
Bincike ya nuna cutar ta mayar da wasu da suka kamu da ita a Jihar kurame.
Kauyukan da aka ruwaito cutar ta fi kamari a cikinsu, sun hada da Mele da Dungundun da Kanya Arewa da Dantanoma da suke a yankunan Kananan Hukomin Babura, Gumel, Maigatari da kuma Sule-tankarkar.
Aminiya ta gano sama da mutum 360 ne suka kamu da cutar a fadin Jihar, sannan kimanin 100 daga ciki sun rasu a sakamakonta.
Dakacin Dungundun, Malam Alkasim Yakubu, ya ce “Cutar ta kashe mutum 19 a yankinmu wanda galibinsu yara ne.”
Ya ce cutar ta kunno kai ne a karshen Afrilu, amma a watan jiya ta ci gaba da yaduwa, sannan ta tsananta a ’yan makonnin da suka gabata.
A kauyen Mele kuwa, mutum 30 suka kamu da cutar, sanna 21 daga ciki sun rasu, kamar yadda Dakacin garin, Malam Yusuf Ahmad ya shaida wa manema labarai.
Bugu da kari, mutum 70 ne aka ce sun kamu da cutar a kauyen Kanya da ke Karamar Hukumar Babura, yayin da ta hallaka mutum 19 daga ciki, inji Dakacin garin, Alhaji Akilu Dawaki.
Akilu Dawaki ya ce, “Matakin da ya taimaka mana wajen takaita yaduwar cutar shi ne, samar da wurin killace wadanda suka kamau da cutar da muka yi.”
According to him “what helps us in controlling the disease was we locally established an isolation center and move the patients”.
Jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Malam Samaila Mahmud, ya tabbatar da barkewar cutar a Jihar.
Sai dai, jami’in ya ce baki daya mutum 257 ne suka kamu da cutar, yayin da cutar ta kashe mutum 65.
Ya ce annobar ta shafin kananan hukumomi 18 ne daga cikin Kananan Hukumomi 27 da Jihar ke da su.