✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Sankarau: Miliyoyin yara suna fuskantar barazana a jihohi 33

Miliyoyin yara a Najeriya na fuskantar barzana saboda jihohi da dama ba su biya kudiin tallafinsu ba wanda zai sa su shiga cikin jerin jihohin…

Miliyoyin yara a Najeriya na fuskantar barzana saboda jihohi da dama ba su biya kudiin tallafinsu ba wanda zai sa su shiga cikin jerin jihohin da za su ci moriyar tallafin rigakafin cutar sankarau da gwamnati za ta gudanar a kwanannan.
Cutar saukarau tana daya daga cikin cututtukan da ke saurin kashe kananan yara ’yan kasa da shekaru biyar a duniya a kasar. Al’ummomi da yawa sun ga yadda aka rika samun barkewar annobar cutar a yankunansu. Kusan sau 166 annobar cutar sankarau ta barke a kananan hukumomi 140 da ke kasar a shekarar 2015 kacal. Sannan a shekarar da ta gabata annobar cutar ta auku sau 183.