✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Murar Tsuntsaye: Manoman Kano sun tafka asarar N600m a watanni 2

Rahotanni dai sun ce tun bayan barkewarta, cutar ta kassara gidajen gona 42 cikin watanni biyu a jihar.

Masu gidajen gona a jihar Kano sun ce sun tafka asarar da ta haura ta Naira miliyan 600 tun bayan barkewar cutar Murar Tsuntsaye a jihar.

Rahotanni dai sun ce tun bayan barkewarta, cutar ta kassara gidajen gona 42 cikin watanni biyu a jihar.

Reshen Kungiyar Masu Gidajen Gona na Najeriya (PAN) a jihar ne dai ya tabbatar da barkewar cutar kusan watanni biyu da suka gabata.

Shugaban kungiyar, Alhaji Umar Usman kibiya ya ce manoman ne suka fara kai rahoton cutar ga hukumomi bayan ganin wasu alamunta a jikin kajinsu.

A cewarsa, tun daga lokacin kungiyar da kuma jami’an Ma’aikatar Noma ta jihar ke aiki ba dare ba rana wajen maganceta.

Alhaji Umar ya kuma ce ya zuwa yanzu, gonaki 42 ne lamarin ya shafa, yayin da aka aike da samfura 40 na wasu kajin domin yin gwaji.

Ya kuma ce hukumomi sun sami nasarar hallaka jimlar kaji 223,695 a gonakin dake sassan da lamarin ya shafa.

“Mun aike da rahoton cutar kimanin watanni biyu da suka gabata, kuma tun lokacin ake kokarin dakileta. An samar da jami’an lafiya na kar-ta-kwana sanye da kayayyakin kariya domin su sami damar yaki da cutar yadda ya kamata.

“Sama da kaji 200,000 ne aka kashe a hukumance a gidajen gona 42 da cutar ta barke,” inji shi.