Daga Hudubar Sheikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi
Godiya da taslimi.
Bayan haka, ku bi Allah da takawa matukar binSa da takawa, wanda ya ji tsoronSa Zai kiyaye shi, Ya jibinci al’amuransa a duniyarsa da Lahirarsa. Allah Madaukaki Ya ce: “Wanda ya dogara ga Allah, to Shi ne Ma’ishinsa.” (dalak:3)
Ya ku Musulmi! Ku yi tunani kan cututtuka masu halakarwa da annoba mai ruguzarwa da kazaman abubuwa masu jawo cuta da hadarurruka masu darkakewa. Ta yaya mutane za su kauce wa abin da ke kawo su, su tanadi magungunansu, su yi wa kansu rigakafinsu, su kubuta daga cututtukan da za su riske su?
Ya ku mutane! Mafi girman cuta, ita ce cutar munafunci da dangoginsa. Cuta ce mai hadari da sharri mai girma. Domin takan mamayi zuciya ta kashe ta, sai ma’abucinta ya zamo rayayye amma matacce. Mai lafiyar jiki amma mai mataccen ruhi. Allah Madaukaki Ya ce: “A cikin zukatansu akwai wata cuta, sai Allah Ya kara musu wata cutar. Kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna karyatawa.” (k:2:10).
Munafunci mugun cuta ne, cuta ce mai kisa, babu wanda ake jarraba shi da shi sai Musulmi. Amma kafiri ba a siffanta shi da munafunci, domin shi ya bayyana kafirci, kuma kafirci ya kunshi dukkan nau’o’in munafunci.
Hakika muminai sun ji tsoron munafunci, salihan bayi sun girgiza da shi. Buhari ya ce a cikin sahihinsa: “Abu Mulaikah ya ce: “Na riski talatin daga cikin sahabbai kowannensu yana jin tsoron munafunci a kansa.”
Amirul Muminina Umar dan Khaddabi (RA) ya ce wa Huzaifa (RA): “Don Allah ka gaya min shin Manzon Allah (SAW) ya ambace ni a cikin munafikai?” Ya ce: “A’a. Kuma ba zan sake tsarkake wani ba a bayanka.” Ma’ana ba zai sake amsa wa duk wanda ya tambaye shi kan sunayen munafikai ba, sai dai hakan ba yana nufin baya ga Umar sauran sahabbai munafikai ba ne.
Hasanul Basri (RH) ya ce: “Mumini ba ya amincewa da munafunci a kansa.” Sannan Imam Ahmad (RH) ya ce: “Wane ne zai amince da munafunci?”
Duk wanda ya kubuta daga munafunci hakika ya kubuta daga sharrorin duniya da azabar Lahira. Wanda ya fada cikin masu aikata munafunci ya yi asara duniya da Lahira. Allah Madaukaki Ya ce kan munafikai: “Kada dukiyarsu da ’ya’yansu su ba ka sha’awa, iyaka Allah Yana nufin Ya yi musu azaba ne da su a rayuwar duniya, rayukansu su fice (su mutu) alhali suna kafirai.” (Tauba: 55).
Munafunci nau’i biyu ne: Nau’i na farko, munafuncin kudiri (akida). Wannan yana fitar da mutum daga da’irar Musulunci. Munafuncin kudiri yana nufin, mutum ya kudirta abin da yake warware Musulunci koda ya yi aiki da rukunan Musulunci da gabbansa. Domin Allah ba Ya karbar ayyuka sai wadanda suka kasance a bisa imani. Munafuncin kudiri kuwa shi ne mutum ya bayyana Musulunci ya boye kafirci. Allah Madaukaki Ya ce: “Daga cikin mutane akwai wanda yake cewa: “mun yi imani da Allah da Ranar Lahira,” alhali kuwa su ba masu imani ba ne. Suna yaudarayya da Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kawunansu, alhali ba su sani.” k:2:8-9).
Ma’abucin munafuncin kudiri mai tabbata ne a wuta, Allah Ya yi mana tsari! Allah Madaukaki Ya ce: “Ranar da munafikai maza da munafikai mata za su ce wa wadanda suka yi imani, “ku dakata mana mu rika amfani da haskenku.” Sai a ce, “ku koma bayanku ku nemo wani hasken.” Sai a sanya shamaki a tsakaninsu da wata katanga wadda ta cikinta akwai rahama, ta bayanta (inda munafukan suke) akwai azaba. Suna kiransu cewa, “ashe ba mu kasance tare da ku ba?” Sai suka ce, “eh, (kun kasance), amma ku kun fitini kanku, kuka shantake, kuma kuka yi shakka, kuma dogon buri ya rude ku har al’amarin Allah ya zo, kuma mai rudin nan ya rude ku game da Allah. Don haka a yau ba a karbar fansa daga gare ku, ko daga wadanda suka kafirta. Makomarku wuta ce, ita ce majibinciyarku, tir da wannan makoma.” (Hadid:13-15).
Ma’abuta ilimi sun binciki hujjojin da ke cikin Alkur’ani da Hadisi sun nazarci nassoshin da suka yi magana kan munafucin kudiri da ke fitar da mutum daga da’irar Musulunci, sai suka samu munafuncin kudiri shi ne: kyama da kiyayya ga Annabi (SAW). Duk wanda yake kin Annabi Muhammad (SAW), hakika ya kafirta koda ya yi aiki da rukunan addini. Allah Madaukaki Ya ce: “Idan wani kyakkyawan abu ya same ka yana bakanta musu rai, kuma idan musiba ta shafe ka, sukan ce, “mun kame al’amarinmu a gabani, sai juya alhali suna masu farin ciki.” (Tauba:50). Kuma Madaukaki Ya ce: “Su ne makiya ka yi saunarsu, Allah Ya la’anme su, yaya ake karkatar da su?” (Munafikun:4). Makiyi shi ne mai yin bakin ciki kan abin farin ciki, kuma ya yi farin ciki kan abin bakin ciki, mai kin ni’ima ta same ka.
Kuma daga cikin munafuncin kudiri akwai: kyama da kin abin da Annabi Muhammad (SAW) ya zo da shi. Allah Madaukaki Ya ce: “Wadanda suka kafirta tir da su, kuma aikinsu ya baci. Wannan saboda suna kin abin da Allah Ya saukar, sai Ya bata aikinsu.” (Muhammad: 8-9). Kuma Madaukaki Ya sake cewa: “Kuma suka yi kira “Ya Maliku! Ubangijinka Ya sassauta mana. Ya ce lallai ku masu tabbata ne a cikinta. Hakika Mun zo muku da gaskiya, sai dai mafi yawanku masu kyamar gaskiya ne.” (Zukhrufi: 77-78).
Daga cikin munafuncin kudiri wanda ke kafirta mutum akwai: karyata Annabi Muhammad (SAW). Allah Madaukaki Ya ce: “A cikin zukatansu akwai wata cuta, kuma sai Allah Ya kara musu wata cutar, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka ksance suna karyatawa.” (k:2:10). Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Idan aka saukar da wata sura, daga cikinsu akwai mai cewa wane ne daga cikinku wannan ta kara masa imani? Amma wadanda suka yi imani, sai ta kara musu imani, sai su rika yin farin ciki. Amma wadanda akwai cuta a cikin zukatansu, sai ta kara musu kazanta a kan kazantarsu sai su mutu suna kafirai.” (k:9:124-125). karyatawarsu ta kara musu kazantar munafunci da zunubi.
Har wa yau daga cikin munafuncin kudiri da ke warware Musulunci akwai: karyata wani abu daga cikin abubuwan da Annabi Muhammad (SAW) ya zo da su, ko nuna kyama ga wani abu daga cikin abubuwan da ya zo da shi. Allah Madaukaki Ya ce: “Shin za ku yi imani da sashin Littafin ku kafirce wa wani sashi? Ba wani abu ne sakamakon wanda ya aikata haka daga cikinku ba, face kaskanci a rayuwar duniya, kuma a Lahira ana mayar da shi zuwa ga mafi tsananin azaba. Kuma Allah bai zama Mai gafala daga abin da abin da suke aikatawa ba.” (k:2:85).
Kuma Madaukaki Ya sake cewa: “Lallai wadanda suka juya bayansu a bayan shiriya ta bayyana musu Shaidan ne ya kawata musu haka, kuma ya yi musu shifta. Wannan saboda su sun ce ga wadanda suka ki abin da Allah Ya saukar: “Za mu bi ku a cikin wasu al’amura.” Kuma Allah Yana sanin asiransu.” (Muhammad: 25-26). Suna kyama ko kin wasu abubuwa da Musulunci ya zo da su, su yi wasu su so su, Shi kuwa Allah ba Ya raba gaskiya biyu, gaskiya sunanta gaskiya kuma daya ce.
Cutar munafunci (1)
Daga Hudubar Sheikh Aliyu Bin Abdurrahman AlhuzaifiGodiya da taslimi.Bayan haka, ku bi Allah da takawa matukar binSa da takawa, wanda ya ji tsoronSa Zai kiyaye…