Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce mutum 21 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Kyandar Biri a fadin kasar ta kuma yi ajalin mutum daya daga farkon 2022 zuwa yau.
Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, NCDC ta ce, “Kawo yanzu, daga cikin mutum 21 da suka kamu da cutar babu wata alamar cewa sun yada kwayoyin cutar, kuma babu wani sauyi da ya auku dangane da bayanan cutar da kuma yadda ake kula da ita.
- Ma’aikacin da ya shafe shekara 84 yana aiki a kamfani daya
- Kotu ta aike da yaran da suka kashe tsoho mai shekara 70 kurkuku
Hukumar ta ce Kyandar Biri cuta ce da ake samun ta a kasashen Afirka irin su Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da kuma Najeriya.
Duk da dai a yankin Afirka take yawo, cutar ta daga hankalin duniya bayan da aka gano sama da mutum 200 dauke da kwayar cutar a tsakanin kasashen duniya 19, akasari a Turai da Gabas ta Tsakiya a farkon watan Mayu. Sai babu asarar rai ko guda da aka samu.
A cewar NCDC, daga cikin mutum 61 da ake zargin suna dauke da kwayar cutar tun daga 21 ga Janairu, an tabbatar da mutum 21 sun kamu da cutar kana mutum daya ya rasa ransa.
Lamarin ya shafi wasu jihohin kasar nan tara ne hade da birnin tarayya, Abuja.