✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Kwalara ta kashe mutum 7 a Binuwai

Akalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a sakamakon kamuwa da cutar Kwalara a Karamar Hukumar Agatu ta Jihar Binuwai. Kwamishinan Lafiyar Jihar, Dokta Joseph…

Akalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a sakamakon kamuwa da cutar Kwalara a Karamar Hukumar Agatu ta Jihar Binuwai.

Kwamishinan Lafiyar Jihar, Dokta Joseph Ngbea ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Makurdi, babban birnin Jihar.

Dokta Ngbea ya ce an tanadi dukkanin kayayyaki da magungunan da ake bukata domin shawo kan lamarin a babban Asibitin Obagaji da ke Agatu.

Kwamishinan wanda ya samu rakiyar babban Sakatarensa, Andrew Amee da Daraktan sashen kula da lafiyar al’umma, Dokta Terna Kur, ya ce an dauki wannan mataki na gaggawa ne biyo bayan sakin kudi da Gwamna Samuel Ortom ya yi, don tabbatar da an kula da lafiyar wadanda cutar ta kwantar cikin inganci.

Kwamishinan ya kuma sha alwashin tanadar kayayyakin gwaji a asibitin domin tabbatar da ingancin gano masu dauke da cutar cikin gaggawa.

Ya yi kira da Majalisar Kananan Hukumomin Jihar da su tallafawa kungiyoyin kiwon lafiya musamman domin amfanin mazauna karkara.

Ya kuma jajantawa mutanen Agatu kan asarar rayukan mutum bakwai da cutar Kwalara ta yi musu sanadi yayin da kuma ya bukaci masu kula da asibitin da su gabatar da bukatunsu a hukumance na inganta ginin asibiti da sauran ababen da suka dace.

Mukaddashin Jami’in Kula da Asibitin, Dokta Adebo Oche, ya yi bayanin cewa an samu jimillar mutum 51 da suka kamu da cutar Kwalara daga Obagaji, da Alokpa da Edeje da Abube doriya a kan mutum bakwai da suka rasu.