Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Osun ta ce akalla mutum uku ne aka tabbatar da rasuwarsu a yankin Ede na jihar bayan sun kamu da cutar Kwalara.
Kakakin Rundunar, SP Yemisi Opalola wacce ta bayyana hakan ga ‘yan jarida ranar Talata a Oshogbo ta kuma karyata rade-radin da ake cewa cin abinci mai guba ne ya kashe su.
- Kwana 1 bayan gobarar kasuwa, wata ta sake tashi a Jami’ar Katsina
- ‘Akwai yuwuwar Najeriya da Yemen Da Sudan ta Kudu su fuskanci fari a bana’
Ta ce sam babu kamshin gaskiya a batun cewa wasu ne suka ba mutanen wadanda dukkansu mabarata ne abinci mai ɗauke da guba a yankin Oke-Gada dake Ede.
SP Yemisi ta ce binciken ’yan sanda na farko-farko ya gano cewa cutar ta Kwalara ce ta kashe su.
“Sai da Baturen ’yan sanda na yankin ya ziyarci gidan Sarkin Hausawa na yankin saboda ba su kai rahoton batun ga ’yan sanda da farko ba.
“Sarkin ya tabbatarwa da ’yan sandan cewa Kwalara ce ta kashe su ba guba ba. Yanzu haka kuma wasu na can kwance a asibiti suna samun kulawa,” inji ta.
Sai dai kakakin ta ce za su ci gaba da bincike a kan lamarin.