Gwamnatin jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar mutum 10 sakamakon cutar Kwalara, yayin da wasu 2,373 suka kamu da ita cikin wata shida a jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Habu Dahiru, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Gombe ranar Alhamis.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 7 a Borno
- Jami’an tsaro sun yi kamen masu sayar da sabbin kudade a Kano
Ya ce a watan Yuni na wannan shekarar 2022 an samu bullar cutar a karamar hukunar Balanga, amma saboda kokarin gwamnati an shawo kan ta.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta bakin Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta jihar, Dokta Abdurrahaman Shu’aibu, inda ya ce an sami barkewan cutar ne sakamakon yawaitar ambaliyar ruwa da aka rika samu a wasu sassan jihar musamman a unguwani 8 a kananan hukumomin Balanga da Yamaltu-Deba da Nafada da Funakaye da kuma Gombe.
Yace tuni Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta dauki matakin dakile cutar inda ko a ranar Laraba aka sami wasu mutum uku da suka kamu da cutar, wasu shida kuma suka mutu a unguwar Kagarawal a Gombe wanda adadin wadanda suka kamu da ita yanzu ya karu zuwa mutum 236.
A cewarsa, yanzu haka an samar da cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar guda 13 a kananan hukumomin biyar din kyauta.
Ya kara da cewa za a shiga gida-gida a rika ba su kwayar maganin cutar wanda zai tsabtace musu ruwan sha a dukkan yankunan da cutar ta bulla.
Habu Dahiru, ya kara da cewa za kuma a gudanar da feshi da kuma tsabtace duk rijiyoyin burtsatse na yankunan al’ummar da aka samu bullar cutar.
Sannan ya ce Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya samar da duk wasu abubuwa da ake bukata domin shawo kan cutar a wuraren da ta bulla.