✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona ta sake yaduwa zuwa Aljeriya, Brazil da Faransa

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana ta bayyana fargabarta ga  Najeriya sakamakon bullar cutar a Nahiyar Afirka, kamar yadda aka samu rahoton cutar ranar Laraba…

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana ta bayyana fargabarta ga  Najeriya sakamakon bullar cutar a Nahiyar Afirka, kamar yadda aka samu rahoton cutar ranar Laraba a kasar Brazil.

A Faransa an samu rahoton mutuwar wani sanadiyyar kamuwa da cutar.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Aljeriya, ta sanar da rahoton bullar cutar Kurona. Yayin da a karon farko aka samu bullar cutar da ake kira COVID-19 a Nahiyar Afirka a kasar Masar.

Jim kadan, an samu bullar cutar karon farko a Kudancin Amurka a kasar Brazil, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar.

A ranar Laraba an tabbatar da bullar cutar ta kama mutum 81,109 a duk duniya, yayin da aka samu rahoton karin yaduwar cutar da ya kai adadin 871 daga ranar Talata zuwa Laraba duk a wannan makon.