✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya

An bayyana damuwa kan zargin cewa babu allurar rigakafin cutar a duk fadin Jihar Kaduna.

Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda take bazuwa cikin sauri a kwanakin nan.

A cewarsa, ’yarsa da ta nuna alamun kamuwa da cutar na kumburin wuya da sarkewar numfashi, an gaggauta mika ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, amma daga bisani ta ce ga garinku nan.

Mallam Bashir ya bayyana cewa, tun bayar rasuwar ’yarsa, a yanzu haka an samu wasu karin yaran uku da suka soma nuna alamun kamuwa da cutar kamar dai yadda ta kasance ga ’yarsa.

Sai dai ya ce ya gaggauta kai rahoton lamarin ga wasu muhukuntan lafiya mafi kusa wadanda suka turo tawagar jamiai da ta soma bayar da allurar riga kafi a yankin.

“Na samu labarin cewa alamun cutar sun bayyana a jikin wasu yaran makwabcina biyu da wata mata a layin da nake zama.”

Ya kara da cewa an kwantar da wasu yaran hudu da su ma suka nuna alamun cutar a wata cibiyar lafiya ta Kakaki da ke kusa da Kwarbai, kuma tuni har an sallami yaro daya.

Ya kuma bayyana damuwa kan zargin cewa babu allurar rigakafin cutar a duk fadin Jihar Kaduna, “wadda na samu labarin cewa sai daga Jihar Neja aka kawo mana ita.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin sakatariyar lafiya ta Karamar Hukumar Zariya, Dokta Hauwa Mahmud, sai dai ba ta amsa kiran da wakilinmu ya yi mata ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.