Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana mutum 11 a matsayin wadanda cutar COVID-19 ta kashe a ranar Juma’a a kasar.
NCDC ta sanar da hakan ne ta shafinta na intanet da safiyar Asabar, inda ta ce kawo yanzu adadin wadanda cutar ta kashe a kasar ya kai mutum 2,211.
Kazalika, cibiyar ta bayyana cewan an samu karin mutum 636 da suka harbu da cutar a ranar Juma’a, wanda ya yi kasa da mutum 117, idan aka kwatanta da 753 da suka kamu da cutar a ranar Alhamis.
Ta ce kawo yanzu jimullar masu dauke da cutar ya kai 181,287 a Najeriya a hukumance.
A cewar NCDC, karin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 din an tabbatar da su ne daga jihohi 16 da kuma Birnin Tarayya.
Jihar Legas, ita ce ke kan gaba da mafi rinjaye na wadanda suka kamu da cutar, inda take da mutum 291, sai Ribas da ke biye mata da 117.
Taraba na da 58, Akwa Ibom na da 54, Kwara 28, Ekiti da Ogun 14 kowaccensu.
Birnin Tarayya na da 13, Oyo 11, Edo guda tara, Osun shida, Bayela na da biyar, Delta da Gombe kowa na da hurhudu, Abiya da Filato na da uku kowaccensu, sai Jihar Sakkwato da ke da mutum daya.
NCDC ta ce daga bullar cutar a Najeriya a watan Fabrairun 2020 zuwa yanzu, an yi wa mutum 2,589,130 gwajin cutar.
Ta kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da jinyar mutum 12,366 a cibiyoyin killace masu ita da aka ware a fadin tarayyar kasar nan.
Ta sake bayyana mutum 149 a matsayin wadanda suka warke daga cutar a ranar Juma’a, kuma an sallame su daga cibiyoyin killace masu cutar COVID-19.
NCDC ta ce kawo yanzu mutum 166,709 ne suka warke daga cutar tun bayan bullarta a Najeriya.