Cutar coronavirus ta bulla a jihar Kogi a karon farko bayan hukumomi sun tabbatar da kamuwar mutum biyu da cutar.
Bullar cutar a jihar na zuwa ne a ranar da aka samu adadi mafi yawa na wadanda da suka harbu da cutar coronavirus a Najeriya.
A karon farko mutum 389 sun kamu da COVID-19 a rana guda a Najeriya a ranar Laraba 27 ga watan Mayu.
A ranar ce kuma cutar ta kashe karin mutum biyar inji sanarwar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).
- ‘Babu’ sauran mai cutar coronavirus a Taraba
- El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
- ‘Yan jarida 10 da ke aiki a ofishin gwamna sun kamu da coronavirus
Alkaluman cutar a Najeriya
Lamarin ya kara yawan alkaluman mutanen da suka harbu zuwa 8,733 tun farkon bullar cutar a Najeriya.
Daga cikin adadin mutun 2,501 sun warke wasu 254 kuma suka riga mu gidan gaskiya.
Hakan ke nuna yanzu mutum 5,978 ne ke fama da annobar a fadin Najeriya.
Alkaluman sun shafi jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihar Kuros Riba ce kada ba a samu bullar cutar a kasar ba.
Sabbin alkaluman COVID-19.
An samu karin masu cutar ne jihohi 23 wanda a cikinsu jihar ke kan gaba da mutum 253 da suka kara kamuwa.
Sauran jihohin su ne Katsina (23), Edo (22), Rivers (14), Kano(13), Adamawa (11), Akwa Ibom (11).
Sauran su ne Kaduna(7), Kwara (6), Nasarawa (6), Gombe (2), Plateau (2), Abia (2), Delta (2).
Akwai kuma Benue (2), Niger (2), Kogi (2), Oyo (2), Imo (1), Borno (1), Ogun (1), Anambra (1).