✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cristiano Ronaldo ya sake lashe Gwarzon dan kwallon Duniya

A ranar Litinin da ta gabata ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal, Cristiano Ronaldo ya sake lashe…

A ranar Litinin da ta gabata ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal, Cristiano Ronaldo ya sake lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Duniya (da aka fi sani da Ballon D’or) a karo na biyu a jere. Sannan wannan shi ne karo na uku da dan kwallon ya lashe kyautar.

Idan za a tuna, dan kwallon ne ya lashe kyautar a bara ga shi ya sake lashe wa a wannan karo.
Shi dai Ronaldo ya fatata a gasar ce tare da dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Lionel Messi da kuma golan Jamus da ke buga kwallonsa a kulob din Bayern Munich na Jamus, Manuel Neuer.
dan kimanin shekara 29 Ronaldo ya karbi kyautar ce daga wurin tsohon dan kwallon Arsenal Theirry Henry wanda ya shafe kimanin shekara 20 yana buga kwallo a kulob daban-daban amma dai Henry ya fi shahara ne a kulob din Arsenal a lokacin da yake kwallo.
Kyaftin-kyaftin din kungiyoyin kwallon kafa na kasashe daga sassan duniya da masu horar da kasashe da kuma ’yan jarida ne suka gudanar da zaben.
Ronaldo ya samu kashi 37 da doriya daga cikin 100 na yawun kurin’un da aka kada ne yayin Lionel Messi ya samu kashi 15 da doriya haka shi ma golan Jamus Neuer ya samu kashi 15 da doriya daga cikin 100.
Lionel Messi ne zakara a tarihin gasar, bayan ya lashe sau hudu a jere.
Yanzu dai Ronaldo ya shiga sahun ’yan kwallo bakwai da suka taba lashe gasar sau uku. Daga cikin wadanda suka taba lashe gasar sau uku akwai shugaban Hukumar Shirya Wasan kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) Michel Platini da Ronaldon Brazil da sauransu.
Tuni Ronaldo ya bayyana murnarsa kan wannan nasara da ya samu kuma ya sha alwashin cigaba da kokari don ganin ya sake lashe ta badi idan Allah Ya kaimu