✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar coronavirus

Hukumar Kwallon Kafar Portugal ce ta bayyana cewa dan wasan ya kamu da cutar Coronavirus.

Cristiano Ronaldo, dan wasan kungiyar Juventus da kuma kasar Portugal, ya kamu da cutar coronavirus.

Hukumar Kwallon Kafar Portugal ce ta bayyana cewa dan wasan mai taka leda a Juventus ya kamu da cutar.

Hukumar Kwallon Kafa ta Portugal da ta tabbatar da hakan ta ce, “Ronaldo ya bar wajen atisayen ’yan wasanmu bayan gwaji ya nuna ya kamu da cutar COVID-19; Don haka ba zai buga wasanmu da Sweden ba.”

A ranar Litinin ce aka nuna wani takalmin kwallo da Kamfanin Nike ya kawo wa Ronaldo, wanda ake so ya sa domin murnar zura kwallo 100 ga kasarsa Portugal.