✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: El-Rufai ya umarci ma’aikatan Kaduna su yi aiki daga gida

Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci ma’aikatan da ke kasa da mataki na 14 da su rika aiki daga gida daga ranar Litinin 21 ga Disamba…

Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci ma’aikatan da ke kasa da mataki na 14 da su rika aiki daga gida daga ranar Litinin 21 ga Disamba 2020.

Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ne ya wallafa hakan, a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.

Wannan umarni ya biyo bayan ci gaba da samun masu kamuwa da cutar Covid-19 da ake yi a jihar da kuma kasa baki daya.

Ya bayyana bayyana umarnin a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar a jihar.

“Ya zama tilas kowa yake amfani da takunkumin fuska a duk lokacin da aka fito daga gida, sannan a kauracewa cinkoson mutane,” a cewar El-Rufai.

Aminiya ta gano cewa jihar Kaduna na da mutum 179 da suka kamu da cutar daga cikin mutum 639 aka yi wa gwaji a ranar Asabar.

Yawancin wanda suka kamu da cutar sun fito ne daga kananan hukumomin Kaduna ta Arewa, Birnin Gwari, Kudan, Jema’a, Kajuru, Chikun, Kaduna ta Kudu, Makarfi, Sabon Gari, Igabi da kuma karamar hukumar Zariya.