Shugaban kwamitin kar ta kwana na dakile cutar coronavirus kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da shirin gwamnatin tarayya na kafa cibiyoyin jinya na musamman da killace wadanda suka harbu da cutar a jihohi 36 da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Boss Mustapha ya bayyana hakan ranar talata a Abuja lokacin da yake jawabi ga ‘yan Majalisar Wakilai ta kasa a kan halin da ake ciki a yaki da cutar coronavirus a Najeriya.
Shugaban kwamitin ya bayyana a gaban ‘yan majalisar ne tare da ministan lafiya da shugaban hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta kafa cibiyar daukar samfuri kuma ta dauki ma’aikatan gudanarwa biyu a ko wacce daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Ya kara da cewa a hankali Kano ta kamo hanyar zama jihar da ta fi fama da cutar a arewacin kasar wanda dalilin hakan ne ya sa Shugaba Buhari ya dauki matakan da ya sanar a ranar Litinin 27 ga watan Afrilu.
A cewar Boss Mustafa suna aiki hannu-da-hannu da gwamnatin jihar ta Kano da sauran hukumomi masu fada aji domin gano bakin zaren, a kuma samar da masalaha.