Indonesiya za ta raba wa ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni a kasarta tallafin Dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 500.
Gwamnatin kasar ta ce duk wani ma’aikaci a kasar da albashinsa bai haura Dala 343.64 (kimanin N150,000) ba a wata, zai samu karin albashi a matsayin tallafin COVID-19.
Ministan Masana’antu, Erick Thohir ya ce tallafin wani yunkuri ne na bunkasa tattalin arzikin magidanta da kyautata rayuwarsu a lokacin COVID-19.
Ya bayyana cewa za a ba da tallafin Dala 41 (fiye da N20,000) a duk wata na tsawon wattani hudu ga wadanda za su amfana a dukkan ma’aikatun gwamnati da kamfanoni.
Ministan Kudin Sri Mulyani ya ce kasar ta ware kudaden ne a yunkurinta na rage wa ‘yan kasarta illar da COVID-19 ta yi wa rayuwarsu.
Indonesiya ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki arziki a yankin Kudu maso Gabashin Asiya.