An samu hatsaniya a tsakanin ’yan sanda da wasu matasa a kauyen Sankara da ke karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa ranar Litinin.
Lamarin dai ya faru ne lokacin da jami’an tsaron suka kai samame a kasuwar kauyen, inda suka tarwatsa ’yankasuwar da suka yi kunnen uwar shegu da dokar da gwamnatin jihar ta kafa ta hana kasuwanci da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.
Wannan ne ya sa wasu matasa suka fusata suka hau jifan ’yan sandan da duwatsu da turakun dabbobi yayinda ’yan sandan suka mayar da martini da hayaki mai sa hawaye.
- Coronavirus: ‘Abin da ya sa Jigawa ke kula da wadanda suka kamu’
- ’Yar shekara 15 ta kashe kanta a Jigawa
Wani ganau wanda ya bukaci a sakaya sunan shi ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ’yansanda sun bude wuta a kan matasan har suka harbi wani yaro dan shekara 10 a gefen kansa, lamarin da ya sa matasan suka tsere kuma kasuwar ta baje.
Sai dai kakakin Rundunar ’Yan sanda ta jihar SP Abdu Jinjiri, ya musanta maganar harbin yana cewa karya ce tsagwaronta aka shirya don a bata wa jami’an tsaron suna.
Ya ci gaba da cewa jefe-jefen da matasa suka yi ne a kan ‘’yan sanda ya shafi yaron domin babu yadda za a yi harsashi ya taba mutum a ka kuma ya rayu.