Bukukuwan Ista na bana ba su zo wa Kiristoci kamar yadda suka saba ba—inda za su tafi majami’u su yi addu’o’i da sauran nau’ukan na ibada.
A bana, sakamakon shawarwarin jami’an kiwon lafiya da dokar takaiata fita ko tarurruka na al’ada ko na addini da rufe kasuwanni da kuma nisantar cunkoson jama’a da gwamnatoci a matakan tarayya da wasu jihohi suka ayyana, Kiristoci a kudancin Kaduna kamar takwarorinsu a wasu sassan Najeriya, a gidajensu suka yi bukukuwan.
A ranar Lahadi, dukkanin coci-coci da ke ciki da gefen garin Kafanchan inda wakilin Aminiya ya zagaya sun kasance a kulle ne, kamar yadda ba a kiran sallah a lokutan salloli biyar na yini a masallatan garin, kuma ba a taruwa don sallar Juma’a saboda dokar da gwamnatin jihar ta kafa.
Wasu Kiristoci da Aminiya ta zanta da su sun bayyana irin halin da suka tsinci kansu a ciki, da yadda suka gudanar da bukukuwan Ista a gidajensu.
- Coronavirus: Gwamnan Legas ya yi addu’ar Easter a gida
- Kayyade ranakun cin kasuwa na jawo mana asara —’Yan tumatur
Wani mazaunin Kafanchan, Joel Adebgoyega, wanda shi ne sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) bangaren matasa, ya ce ya gode Allah duk da kasancewar a gida ya gudanar da bikin tare da iyalinsa, amma ya gudanar da makamancin hakan tare da abokansa Musulmai ta kafofin sada zumunta, inda suka yi musayar sakwanni da juna.
“Bikin Ista cikar sakon Isa Almasihu ne a bayan kasa. Na gudanar da bikin na bana ne tare da iyalina a gida, inda na yi amfani da wannan damar wajen koya wa yarana wakokin Ista, na yi wasannin Ludo da matata sannan na saurari labarai musamman na halin da ake ciki game da cutar COVID-19 inda a karshe muka yi wa kasarmu addu’a don a fita daga cikin wannan hali da muka tsinci kanmu da sauran kasashen duniya,” inji Mista Adegboyega.
An ji jiki
Ya kuma ce ta bangaren kasuwanci ya yi asarar cinikin da ya saba yi a irin wannan lokaci domin yana aikin buga kati ne wanda bai samu damar yin ko daya ba a wannan karon, sannan kuma ya mallaki makaranta mai zaman kanta da ta kunshi sashen nursery da firamari da kuma sakandiri wanda sai lokacin jarabawa yawancin iyaye ke biyan kudin makarantar ‘ya’yansu amma lura da yadda aka kulle makarantu tashi daya ya sa da yawan iyaye ba su biya ba.
“Ka ga dole in ji jiki ai,” a cewarsa.
Ita kuwa Fasto Ngozi Olukola ta cocin Elshaddai International da ke Kafanchan cewa ta yi damuwarta kawai ita ce yadda ta rasa haduwa da sauran ‘yan uwa don musayar farin cikin wannan ranar.
Amma a cewarta, a daya bangaren babu abin da ta rasa domin Yesu Almasihu da suke taron dominsa ba a killace yake ba kuma wannan dokar ba ta shafe shi ba.
Yanayi na daban
Shi kuma Fasto Michael Ibrahim Maikarfi, shugaban kungiyar CAN reshen karamar hukumar Sanga, ya nuna godiyarsa ne ga Allah da ya ba shi lafiyar gudanar da hidimar Ista Iduk da ba a yi ta yadda aka saba ba, yayinda wasu ke fama da cutar coronavirus a sassa daban-daban na duniya.
“Duk da cewa bana mun yi hidimar Ista ne cikin wani yanayi na daban sanadiyyar annobar COVID-19, wadda ta sa muka yi sanarwa shugabannin ikilisiyoyinmu cewa kowa ya zauna ya gudanar da sujjadarsa a cikin gida tare da iyalinsa maimakon zuwa masujjada.
“Zumunta da addu’o’in da iyalai suka yi a cikin gidajensu shi ma abu ne mai kyau, domin ko Yesu Kiristi a lokacinsa ya kasance yana bin mutane gida-gida domin dada zumunta da yin addu’o’i tare da su kamar yadda ya zo cikin a cikun Baibul cikin littafin Matta sura ta 18 aya ta 20 an nuna cewa duk inda mutum biyu zuwa uku suka hadu cikin sunan Yesu to Allah na tare da su, don haka imaninmu shi ne addu’o’in da muka yi a cikin gidajenmu sun samu karbuwa a wajen Allah”.
Bikin ya zo a hagunce
A karshe ya yi kira ga mabiya da su ci gaba da yin biyayya ga hukumomi da shawarwarin masana kiwon lafiya don samun mafita daga wannan annobar.
Rabaran A.A. Abutsa, shugaban Cocin Baptist ta Daya da ke garin Gwantu, hedkwatar karamar hukumar Sanga, cewa ya yi duk da bikin Ista na bana ya zo musu ne a hagunce, amma sun yi imani da kaddara kamar yadda ya zo cikin littafin Baibul cewa su kasance masu godiya ga Allah a duk halin da suka tsinci kansu a ciki.
“Duk da mawuyacin halin da ake ciki da kowa da kowa ke kokawa, hakan wata dama ce ta kusantar Allah da kuma kyautata alaka tsakanin iyalai da makwabtansu da kuma tsakanin shugabanni da mabiyansu”, inji shi.