Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 1,182.
Adadin dai ya kai haka ne bayan da aka samu sababbin kamuwa da cutar har mutum 87.
Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter ne suka nuna hakan.
“Zuwa karfe 11.55 na daren 25 ga watan Afrilu akwai mutum 1,182 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, inji NCDC.
Haka kuma yawan wadanda suka rasu ya karu da mutum uku.
Talatin da uku daga cikin mutanen da suka kamu a baya-bayan nan a jihar Legas suke, 18 a Borno, 12 a Osun, tara a Katsina, hudu a Kano da Ekiti sai uku a Edo da Bauchi da kuma daya a Imo.
A cewar NCDC, daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu mutum 222 aka sallama, yayin da 35 suka riga mu gidan gaskiya.
Zuwa tsakar daren na 25 ga wata dai an tabbatar da samun mutanen da suka kamu da COVID-19 a jihohin Najeriya 28 da Yankin Babban Birnin Tarayya.