Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana cewar ba a samu rahoton ɓullar cutar ƙyandar biri a jihar ba.
Amma, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa, gwamnatinsa ta shirya tsaf don tunkarar cutar tare da daƙile ta.
- Bana neman kujerar Tinubu a 2027 — Ganduje
- Tinubu ya rage yawan tawagar da za ta halarci taron MDD a Amurka
Ya yaba wa Cibiyar Daƙile Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) bisa ɗaukar matakan da suka dace don hana yaɗuwar cutar.
Gwamnan, ya kuma jaddada cewa NCDC tare da haɗin gwiwar hukumomin lafiya na jihohi suna sanya ido sosau kan cututtuka a jihar tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa jihohin sun shirya tunkarar ɓarkewar cutar, tarw da haɗin gwiwar NCDC.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labaran gwamnatin jihar, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, ya Gombe na da cibiyoyin gwaje-gwaje da ɗakunan bincike guda huɗu da ke jiran ko-ta-kwana.
A ranar Lahadi ne, NCDC ta ayyana ɓarkewar cutar ƙyandar biri a faɗin Najeriya.
Cibiyar ta ce yanzu haka akwai mutum 39 da suka kamu da cutar, kuma jihohin Bayelsa, Kuros Riba, da Jihar Legas na gaba wajen wuraren da aka fi samun masu kamuwa da cutar.