Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya zuwa tsakar daren Laraba ya kai 873, a cewar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC.
Hukumar, wadda ta fitar da alkaluma na baya-bayan nan na wadanda ta tabbatar da kamuwarsu a shafinta na Twitter, ta ce adadin ya kai haka ne bayan samun sabbin kamu sama da casa’in.
“An samu sabbin wadanda suka kamu da COVID-19 mutum 91”, inji hukumar, wadda ta kara da cewa 74 a cikinsu a jihar Legas suke, biyar a Katsina, hudu a Ogun, biyu a Delta, biyu a Edo, daya a Kwara, daya a Oyo, daya a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Adamawa.
Hukumar ta kuma ce zuwa karfe 11.25 na daren 22 ga watan Afrilu, an sallami mutum 197 daga cikin 873 da aka tabbatar sun kamu, yayin da 28 suka riga mu gidan gaskiya.
- Coronavirus: Jigawa ta karbi almajirai 524 daga Kano
- Yadda za a yi da Muslumin da coronavirus ta yi ajalinsa
A yanzu haka lissafin adadin wadanda aka tabbatar sun kamu a jihar Legas ya kai 504, na Abuja 119, na Kano kuma 73.
Adamawa ce dai jiha ta baya-bayan nan da aka samu wanda ya kamu; kuma gwamnatin jihar ta ce mutumin ya dawo ne daga Kano.