✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohuwa mai shekara 90 ta fara amfani da rigakafin COVID-19 na Pfizer

Wata tsohuwa mai kimanin shekaru 90 ta zama mutum ta farko da ta fara amfani da rigakafin COVID-19 ta kamfanin Pfizer-BioNTech.

A ranar Talata kasar Birtaniya ta fara aiwatar da shirin rigakafi mafi girma a tarihinta, inda wata tsohuwa mai kimanin shekara 90 ta zama mutum ta farko da aka yi wa allurar rigakafin COVID-19 na kamfanin Pfizer-BioNTech.

Yayin gwajin mai cike da tarihi da ya gudana a yankin Coventry na kasar, Margaret Keenan ta kasance wacce aka fara yi wa sabon rigakafin.

A makon jiya ne Birtaniya ta zama kasa ta farko da ta amince da rigakafin na kamfanin Pfizer-BioNTech, lamarin da ya kara karfafa gwiwa a yakin da ake yi da annobar da kawo yanzu ta hallaka sama da mutum miliyan daya da rabi a duniya.

Birtaniya na daya daga cikin kasashen da annobar ta fi yi wa illa inda kusan mutum 61,000 suka mutu, sama da miliyan daya da dubu 600 kuma suka kamu.

Sakataren Lafiya na kasar, Matt Hencock, ya bayyana fara amfani da rigakafin a matsayin wani babban ci gaba a yaki da cutar, yana mai cewa hakan zai kare mutane da dama.