Cutar COVID-19 ta hallaka ’yan majalisa 32 a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango, adadin da ya kai kimanin kaso biyar cikin 100 na yawan ’yan majalisar kasar.
Hukumomi sun ce hakan dai na nuni ne da irin mummunar illar da cutar ke ci gaba da yi a sassa da dama na duniya.
- An hana dalibai masu zanga-zanga zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna
- Real Madrid ta sake daukar Ancelotti a matsayin sabon Koci
Kazalika, adadin na kuma karuwa ne yayin da kasar ke kokarin samun rigakafin cutar a bangare daya, yayin da a daya bangaren kuma take fama da matsalar duwatsu masu aman wuta.
A makon da ya gabata dai Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Kasar, Jean-Marc Kabund ya ce, “Wannan annoba na yin matukar illa a kasarmu, dubban mutane ne ke mutuwa a kulli-yaumin saboda ita.”
Kwango dai wacce daya ce daga cikin kasashen da suka fi yawan jama’a a nahiyar Afirka na da mutane sama da miliyan 86, kuma ta sami sama da mutane 31,000 da suka kamu da cutar, 786 kuma aka tabbatar da rasuwarsu.
A watan Maris din 2021 da ya gabata, kasar ta karbi rigakafin cutar ta COVID-19 samfurin AstraZeneca kimanin miliyan daya da dubu 700.
Sai dai ko an jinkirta fara amfani da ita har zuwa tsakiyar watan Afrilu saboda yadda kasashe da dama a nahiyar Turai suka dakatar da amfani da ita sakamakon daskarewar jinin da take haifarwa.
Ya zuwa ranar Juma’ar da ta gabata, sama da mutum 23,000 ne aka yi wa rigakafin a kasar, kuma yawancinsu a babban birnin kasar na Kinshasa suke, kamar yadda Ma’aikatar Lafiiyar kasar ta tabbatar.