Cutar COVID-19 ta yi ajalin sama da mutum dudu dari biyar a duniyar tun bayan bullarta a watan Disamban 2019.
Kawo yanzu cutar ta fi kamari a Amurka, inda ta hallaka mutum 125,803, kamar yadda alkaluma daga Jami’ar John Hopkins suka nuna.
Fiye da rabin mutum 500,000 da suka rasu daga cutar a duniya sun mutu ne a kasashe biyar, kamar yadda alkaluman suka nuna.
Brazil ce ta biyu wurin yawan mamata sakamakon cutar da mutum 57,622 da ta yi ajalinsau.
Mau biye da Brazil ta fuskar mamata sun hada Birtaniya da Italiya da kuma kasar Andalus.
Jerin kasashen duniya da cutar ta fi yin kisa a cikin kowane mutum miliyan daya na al’ummominsu su ne:
- San Marino – 1,235
- Belgium – 839
- Andorra – 675
- Birtaniya – 639
- Andalus – 606
- Italy – 574
- Swidin – 522
- Faransa – 455
- Amurka – 377
- Holand – 356