Kwamitin da ke yaki da annobar COVID-19 a jihar Kano ya ce akalla mutane 17 ne suka rasu sakamakon cutar cikin makonni shidan da suka gabata a jihar.
Mataimakin Shugaban Kwamitin, Dakta Sabitu Shu’aibu Shanono wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga masu rike da sarautun gargajiya da sauran shugabannin al’umma da ke jihar, ya kuma ce mutum 11 sun rasu ne a watan Disamba, sai kuma shida da suka rasu a watan Janairu.
Ya ce sannu a hankali jihar na dada samun karin masu dauke da cutar, kasancewar adadin masu dauke da ita ya karu da kusan kaso 12.7 cikin 100.
Shanono ya kuma bayyana wasu daga cikin kalubalen da jihar ke fuskanta wajen yaki da cutar da suka hada da karancin bayar da hadin kai daga mutane wajen bin matakan kariya, karancin yarda da wanzuwar cutar, da kuma kin amincewar masu dauke da ita su killace kansu.
Wadanda suka halarci taron dai sun hada da sarakunan Kano da Bichi da Rano da Karaye da kuma na Gaya wanda Makaman Gaya ya wakilta tare da hakimansu.
Kazalika, sarakunan kabilun Ibo da Yarabawa da na Edo su ma sun halarci taron.
Kwamitin dai ya roki masu rike da sarautun gargajiyar da su hada kai da gwamnati wajen taimakawa a dakile cutar, kamar yadda suka yi a farkon barkewarta.