Ministan Harkokin Wajen Zimbabwe, Sibusiso Moyo ya mutu ranar Laraba, kwana daya bayan ya kamu da cuta coronavirus.
Mukaddashin Babban Sakataren Shugaban Kasar kuma dan Majalisar Zartarwar kasar, George Charamba ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa.
- Duk wanda ya shiga jihar Kogi ya kubuta daga COVID-19 – Yahaya Bello
- Wani ya auri ’yarsa ’yar shekara 13 a Zimbabwe
Daya daga cikin iyalan mamacin ma ya tabbatar da rasuwar mamacin ga Kamfanin Dillancin Labaran kasar China, Xinhua.
“Gaskiya ne, dan uwana ya rasu bayan kamuwa da COVID-19 a jiya,” a cewar daya daga cikin iyalan mamacin.
Mista Sibusiso dai shi ne babban jami’in gwamnatin kasar na uku da ya rasu sakamakon cutar, tun farkon shigarta kasar a watan Maris din 2020.
Ministan, wanda tsohon soja ne, na daya daga cikin wadanda suka jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin tsohon Shugaban Kasar, marigayi Robert Mugabe a watan Nuwamban 2019.
Daga bisani ne kuma Shugaban Kasar mai ci, Emmerson Mnangagwa ya nada shi a matsayin daya daga cikin ministoci a gwamnatinsa.