Babban Kwamandan Runduna ta 6 ta Sojin Kasa ta Najeriya da ke Fatakwal, Jihar Ribas Manjo Janar Olu Irefin ya kwanta dama.
Janar din sojan din ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.
- Maharan da suka je garkuwa da magidanci sun dauke matarsa
- An rage farashin Data da kashi 50 a 2020 a Najeriya
- El-Rufai zai dawo da dokar kulle a Kaduna idan…
Janar Olu Irefin, na daga cikin manyan jagorori a rundunar da ke halartar babban taron Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na 2020 lokacin da aka gano ya kamu da cutar.
A safiyar Alhamis runduanr ta sanar da soke abubuwan da suka yi saura a taron da aka fara gudanarwa ranar Litinin.
Rundunar ta kuma umarci a killace ddukkannmin mahalarta taron na tsawon kwana 14 tare da kiyaye sauran matakan kariyan COVID-19.
Kafin zamansa Babban Kwamandan Runduna ta 6 da ke Fatakwal a watan Yuli, Janar Janar Olu Irefin shi ne Babban Kwamandan Runduna ta 81 da ke Legas.