✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta kashe dan takarar Shugaban Kasar Congo

Cutar ta yi ajalin Guy-Brice Parfait Kolelas a jajibirin zaben.

Cutar coronavirus ta kashe dan takara Shugaban Kasar jam’iyyar adawa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Guy-Brice Parfait Kolelas a jajibirin zaben. 

Kafin rasuwarsa ana gab da zaben shugaban kasar, Guy-Brice shi ne babban dan takara daga bangaren jam’iyyar adawa.

Ya rasu ne a cikin jirgin saman da ya dauke shi daga Brazzaville zuwa kasar Farasna, a yammacin ranar Lahadi, yana da shekara 66 a duniya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne sakamakon gwaji ya ya kamu da cutar coronavirus, inda har ya gaza gudanar da taron yakin neman zabensa  na karshe a birnin Brazaville.

Marigayin ya wallafa hoton bidiyonsa  daga gadon jinyarsa, inda ya shaida wa magoya bayansa cewa, su yi masa fatan alheri.

Kolelas, ya kasance babban dan adawa ga shugaban kasar ta Congo, Denis Sassou Nguesso.

Wasu daga cikin ’yan adawar kasar sun kaurace wa zaben, saboda katse hanyar sadarwa ta intanet da gwamnatin kasar ta yi, wanda suke kallo a matsayin wata hanya ta yin magudi.

Masu sharhi kan al’amuran zabe a nahiyar Afrika na ganin zaben da aka gudanar an fi ba wa Shugaba Nguesso fifiko da dama a zaben.