Mukaddashin Shugaban Jami’ar Ibadan da ke Jihar Oyo, Farfesa Adebola Ekanola ya sanar cewa akalla mutum 10 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a Jami’ar, a yayin da mutane ke nuna halin ko-in-kula ga matakan kare yaduwar cutar.
Farfesa Adebola Ekanola ya bayyana haka ne a ranar Juma’a 23 ga Yuli, 2021 a lokacin da yake jawabi a taron bidiyo da sashen yaki da COVID-19 na Jami’ar ya shirya wa manyyan jami’anta.
Ya ce ko da yake cutar ba ta yiwa Jami’ar ta Ibadan illa ba, akwai bukatar dalibai da malama su rika daukar kwararan matakan kare yaduwarta a Jami’ar, kasancewar illar cutar ta fi kamari a yanzu fiye idan aka kwatanta da farkon zangon karatu a Jami’ar.
Ya kara da cewa an kafa kwamitin hadin guiwa da za ta tabbatar da ganin dalibai da malaman Jami’ar na bin ka’idojin kare yaduwar cutar ta hanyar wanke hannaye da sanya takunkumi da kuma bayar da tazara.
Ko a makon jiya, mahukuntan Jami’ar Legas sun ba da umarnin rufe dakunan kwanan dalibai da ke karatun digiri na farko, suka kuma umarce da su koma gida bayan gano bullar cutar ta COVID-19 a Jami’ar.